Zan yi murabus a mutunce idan lokaci ya yi – Malami

Daga SANI AHMAS GIWA a Abuja

Antoni Janar na Tarayya kuma Ministan Shari’a, Abubakar Malami, ya bayyana cewa ba zai yi murabus daga kujerarsa ba, inda ya bayyana cewa zai kammala wa’adin mulkinsa a mutunce a watan Mayun 2023.

Malami ya bayyana hakan ne jiya Alhamis, 17 ga watan Maris, a Abuja yayin da yake jawabi a wani taro da ƙungiyar masu aiko da rahotanni na shari’a ta ƙasa suka shirya.

Ministan ya yi watsi da rahotannin kafafen yaɗa labarai na cewa ya yi murabus daga kujerarsa, yayin da ya buƙaci manema labarai da su kasance masu gaskiya a rahotanninsu.

Ya kuma yi kira ga hukunta ‘yan jarida da makiran ‘yan siyasa ke amfanin da su.

“Lokaci ya yi da ya kamata mu inganta ilimin kafafen yaɗa labarai domin ‘yan Nijeriya su ji daɗin tantance gaskiyar bayanai.

“Yawancin mutane da suka dogara da wasu masu yaɗa labarai da ba su da ƙwarewa za su yi mamakin ganin cewa Malami da aka ce ya yi murabus daga muƙamin Antoni Janar na Tarayya kuma Ministan Shari’a har yanzu yana gudanar da ayyukansa da suka haɗa da halartar taron Majalisar Zartarwa ta Tarayya a ranar Laraba, yana bayar da damar hira da manema labarai sannan kuma a yau ya buɗe wannan taro a matsayin Antoni Janar na tarayya.

“Akwai ƙarshen komai. Wa’adin mulkina bai riga ya zo ƙarshe ba. Ina addu’ar kyakkyawan ƙarshe,” inji Malami.