2023: Abinda Obasanjo ya shaida min game da shugabancin Igbo – Ohuabunwa

Daga BAKURA MUHAMMAD a Bauchi

A ƙoƙari da ya ke yi na cimma burinsa na kasancewa Shugaban Tarayyar Nijeriya, wani ɗan takara a ƙarƙashin jam’iyyar PDP, Mazi Sam Ohuabunwa, makon da ya gabata ya ziyarci tsohon shugaban ƙasa, Olusegun Obasanjo a garinsu na Abeokuta dake cikin jihar Ogun.

Mai neman takarar shugabancin ƙasar, ya kuma ziyarci dattawa da shugabanni na jam’iyyar PDP dake jihar ta Ogun, a cikin ziyarce-ziyarcen kamun ƙafa da yake yi.

Da yake yi wa manema labarai jawabi, jim kaɗan bayan ganawar su ta sirri da tsohon shugaban ƙasan, Ohuabunwa ya ce, ya je Abeokuta ne domin taya dattijon murnar cika shekaru 85 da haihuwa, ya kuma gwamatse shi da tsare-tsaren sa na neman takarar shugabanci.

Tsohon shugaban na ƙungiyar masu haɗa magunguna ta Nijeriya (PSN), ya ce Obasanjo ya bayyana masa a zahirance cewar, lokaci ne da ya dace ƙabilar Igbo su fito da wanda zai kasance shugaban ƙasa a shekara ta 2023.

Ya ce, “mun yi zantuttuka akan Nijeriya da aniyata ta takarar neman shugabancinƙasa. Ya shaida min cewar, lokaci ne na Kudu maso Gabashin Nijeriya. Saboda haka idan mutane kamar mu suka yunƙuro da buƙatar neman shugabanci, sukan ji ƙwarin gwiwar yin hakan.

“Obasanjo yana da yaƙinin cewa lokaci ya zo da za a wanzar da sasanci a ƙasar Nijeriya. Ya kuma yi yaƙinin cewar, akwai batutuwa masu yawa da Kudu maso Gabas na tattaunawa, fiye da batun son haɗin kan ƙasa.

“Yana kuma da yaƙinin cewar, Kudu maso Gabas za ta gabatar da samfuririn ayyuka nagari da sana’o’i daban-daban waɗanda za su taimaka wajen samar da ayyukan yi, haɗi da yaƙar talauci da ya zama annoba a Nijeriya. A farkon saduwar mu da shi, ya gafatar da jerin ƙalubaloli da zan fuskanta, da kuma yadda zan shawo kan su. Kuma na yi bibiyar waɗannan matsaloli, kuma sun zame min kandagarki.

“Saboda haka, ya shaida min cewa aiki ne mai matuƙar wahala, kuma yana farin cikin ganin yadda na juri wannan tafiya har ya zuwa wannan rana ta yau, tare da duba yadda wannan mafarki nasa na ganin ɗinkakkiyar Nijeriya ta wajen haɗin kai, da kowa da kowa zai yi alfahari da ita cewar, tamu ce zai cika.”

Tsohon shugaban, na kuma ƙungiyar masu sana’o’i (MAN), ya bayyana cewar, hanya mafi sauƙin wanzar da sahihantaccen zaman lafiya a cikin ƙasa mai ɗimbin ƙabilu da yanayin tsare-tsaren zamantakewa daban-daban kamar Nijeriya yana buƙatar yin adalci wa kowa da kowa.

“Kuma mulkin karɓa-karɓa ko kewayawa suna daga cikin hanya na tabbatar da tarayya, da kuma ganin cewar, kowane ɗan Nijeriya yana tutiya da ƙasar sa. Saƙo na shine ɗaukacin dukkan al’ummai da take Kudu su yi tinƙaho da cewar, ƙasar su ce, musamman ‘yan uwana daga Kudu maso Gabas subji a jika, suma halatattun ‘yan Nijeriya ne domin mun bayar da dukkan gudummawa da ta dace tun daga zamanonin baya irin nasu Dr. Nnamdi Azikiwe, har zuwa yau.

“Saboda haka, mu ba baƙi ba ne wa Nijeriya, ba kuma raɓa danni ba ne. Idan kuma ta ɓangaren siyasa ne, wajibi ne mu furta batun haƙƙin mu, na samar wa Nijeriya jagoranci nagari data gaza samu, kuma muna da ƙwarin gwiwar Allah zai bamu wannan damar a shekara ta 2023, kuma ‘yan Nijeriya za su banmu goyon baya da zabmu mayar da Nijeriya shiga cikin ƙasashe na gaba-gaba a duniya, kuma wannan shine muradi na, Nijeriya ta hau tudun tsira mai yin gogayya da kowace ƙasa a duniya, kuma mafi muhimmanci, ƙasa mai yi wa kowa hidima, da samar da ayyuka da sana’o’i wa matasa, su nuna bajinta da firtsi ko kafa sabuwar al’adar su,” inji Ohuabunwa.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *