Rayuwar gidan Pako (1)

Manhaja logo

Assalam alaikum. Da fatan duk mu na lafiya. Allah ya albarkaci jaridar Blueprint Manhaja.

A yau zan rubuta wasiƙa ta ne a kan gidan Pako. Gidan Pako, ku a ce gidan jeka na yi ka, wanda akasarin baƙi ne ke rayuwa a ciki. Pako, ko muce Baca, wuri ne da ba ruwan gwamnati da shi, kuma ba wani sarki ko shugaba. Babu wani ofishin jami’i na tsaro, ko hukuma masu hukunci. Wuri ne da jahili ke mulki da iko, wuri ne mai kuɗi talaka ya fi shi daraja.

Darajar mai kuɗi da kuma darajar talaka, an fi girmama talaka fiye da mai kuɗi. Wuri ne da ’yan ƙungiya suka fi yawa. A wurin ne za ka ga masu ƙungiyar Bulu-bulu, da kuma 77 da kuma 99.

Kowa ka gani a gidan pako wuya ce takai shi, wataƙila ya rasa wurin zama, ko kuma korarsa aka yi daga wani wajen. Kafin mu yi nisa a labarin yaruwar gidan paako, yana da buƙatar mu san mene ne Paako, sannan ya ake gidan paako, sannan wa ke da alhakin sayar da gida ko fili da ake gina gidan paako.

Gidan Paako, gida ne da aka fi samunsa a kudancin Nijeriya. Mafi yawan masu sama a wuraren ’yan bariki ne waɗanda suka je neman gumin su. Mutum ya je gari, kuma bai da wurin zama, sai ya samu wuri kamar bakin teku, ko kango wanda ba a gama kammalawa ba, sai ya biya zauna gari banza kuɗin goro, sannan su ba shi damar zama a ciki.

Shi kuma zai samo Bambu, ko falankin katako ya gyara ɗaki. Ɗakin kamar ƙakunan bakin daga a fagen yaƙi, wanda sojoji ke ke yi da tampal ko tantin. To shi na gidan pako, laida sai samo, ko buhun siminiti, waton algarara, ya shimfiɗa shi ba tare da fulo ko abinda sai rage sanyi ko zafi ba. Wani zubin ma idan ana ruwa, ɗakin na yoyo, shikenan kuma ya tasa madigara. Idan kuma a watan 7 ne, akwai ruwa da aka cika yi a ki wace shekara, wanda ruwan ana masa laƙabi da kwana 7 a watan 7, waton (7July). Ruwa ne da ake yi kwana 7 a jere ba tare da ƙaƙƙautawa ba, sannan masu gida a ƙasa suna ruwa, domin idan mutum ba beni ne da shi ba gaskia yana cikin damuwa.

Musamman ma waɗanda suke cikin tsibirin Legas, da Lekki, da kuma wurin da ake kira ‘Victoria Island’. Ina kuma ga ɗan gidan pako, wanda shi ko fulo babu a ɗakin shi bare kuma ace madakatar sanyi.

A gidan pako, babu asibiti, ko an kai mutum asibiti idan har an gano cewa daga gidan pako yake to rainin da za a nusa masa ma daban. Shi yasa, ma kowa kagani a gidan paako to rayuwar sa yake, kamar ɗan wani sarki.

Masu sayar da filin gidan paako, zauna gari banza ne, wanda Bale yana goya musu baya, sai abinda suka ce sannan kai kuma ka bi. Ana iya sayar da filin gidan paako a farashi mafi tsada, wanda gaskiya idan wasu wurare ne a Nijeriya za ka iya samun fili fuloti guda.

Gidan pako, har Ila yau, waje ne da Gwamnati bata san da ita ba, kamar yadda na fada a farko, mutane na zuwa bakin ruwa, ko wani jeje mafi kusa da gari, ku kango da ba a gama ginawa ba, sai su yi gidan su, sannan sune da ikon wurin. Hatta ko da ace mai filin ne yazo, idan ba su san shi bane, to zagi da kurari za ayi masa. Hakan ya taɓa faruwa a wani gidan pako da ke Maruwa Leeki pace 1.

Mutane sun yin ɗakunan su na gidan pako a filin wani, sun shafe aƙalla kusan shekaru 7, shiko mai filin yana sane. Wata rana ya ɗan je ya zaga yaga filin shi, yana ma wucewa sai wuri ya cushe, yakan ya sa ya yi hon, ba da jimawa ba wani ɗan acaɓa ya jefa masa ashar, abin ya dame shi. Ya rasa mai zai yi, kawai ya ce zai yi gini a wajen, ya kawo jami’an ’yan sanda, da kuma sojoji, suka tashi mutane, ya kewaya filin da katanga. Amman ina, kash, idan har waɗannan zauna gari banza na nan, to gaskia sai sun sayar da fili, kuma sai sun kira mutane su zo su zauna, kuma su karɓi kuɗi mai yawa.

To su wane ne ke zama a gidan Pako? Kamar yadda na yi bayani, baƙi ne ’yan bariki, waɗanda akasarin su sun zo ne daga wata jiha, zuwa wata jihar, wasu ma daga wata ƙasa zuwa wata ƙasar. Kamar nan Nijeriya, zaka gani, akwai ƙasar Nijer, da Kotono, da kuma Gana da Togo, harada ma ’yan Afirka ta kudu, sun samar da wani waje, kuma suka yi gidajen su, tare da makarantun su. Masu mutanen ma acan aka haife su, kuma a pako suka girma, sannan a ciki suka yi karatu.

Gidan Pako, akwai makaranatun katako, sannan kujerun bambu, da kuma fili na wasan yara, da kuma. Yara suna makaranta, kuma makarantar ba ta da rajista da gwamnati, ba a rasa wasu makarantun gidan pakon waɗanda suna da rajista da gwamnati ba, amman yana wuya, koda ma akwai, to gaskia irin karantu ne da suka gaya biyan kuɗin hayar muhalli da suke karatu a ciki. Zan cigaba a mako na gaba.
Wassalam.

Saƙo daga Mohammed Albarno, O8034400338, [email protected]