Zanga-zanga: Ka saurari koken ‘yan Nijeriya, Ndume ya shawarci Tinubu

Spread the love

Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja

Tsohon mai tsawatarwa na Majalisar Dattawa, Sanata Mohammed Ali Ndume, ya buƙaci Shugaban Ƙasa Bola Ahmed Tinubu da ya saurari buƙatun ‘yan Nijeriya waɗanda ke shirin yin zanga-zanga.

Ndume ya yi wannan kiran ne a wata hira da gidan talabijin na Channels TƁ a wani shirin sa mai taken Politics Today.

Da aka tambaye shi ya yi tsokaci kan kiran da shugaban ƙungiyar ƙwadago ta Nijeriya (NLC) Joe Ajaero ya yi wa shugaban ƙasar na ya tattauna da ‘yan ƙasa, Ndume ya ce ya amince da wannan kira.

Ya ce, “Na goyi bayan wannan kira nasa. Shugaban NLC ne ya gabatar da wannan ƙudiri. Ka ce masa ina goyon bayan ƙudirinsa na cewa shugaban ƙasa ya saurari ‘yan Nijeriya.

“Yau kwanaki 26 daga harin da aka kai a Gwoza. Jama’ata suna ta faman ƙoƙarin komawa gona; muna fafutukar tsira. Muna iya ganin gwamnatin jihar da sauran hukumomi suna ƙoƙarin taimaka mana. Muna fama da wannan yanayin; ba mu da lokacin yin zanga-zanga.

“Don nuna rashin amincewa da wa? Ina shakkun ko za a gudanar da zanga-zangar a Maiduguri. Wannan ba wai ina hana mutane su yi kokensu ba ne, tsoro na shi ne kallon abin da ya faru yayin zanga-zangar ta EndSARS.

”Ina fatan ba za ta rikice ta zama rigima ba kuma musamman ma lokacin da ba a don jagorancin ba. Hatta ƙungiyar ƙwadagon da suka yi yajin aiki sau da dama, yanzu kawai muna ganin suna ta fama ln ƙoƙarin gudanar da zanga-zanga. Amma ban san su waye jagororin ba.”

By ukarofi