Zanga-zanga: Masu amfani da wayoyi da motoci ake hari, DHQ ta gargaɗi al’umma

Spread the love

Daga BALA MUHAMMAD

Hedkwatar tsaro ta ƙasa (DHQ), ta ce ta gano wani shiri da wasu ɓata-gari ke yi na kai hari wa masu motoci da masu amfani da manyan wayoyi da kuma mallakar wasu kadarori a cigaba da shirye-shiryen gudanar da zanga-zangar ‘EndBadGovernance’ a za a yi wata mai zuwa.

A ranar Alhamis ne, Daraktan ofishin kan harkokin yaɗa labarai, Manjo Janar Edwerd Buba ya faɗi haka a yayin ganawa da manema labarai a Abuja inda ya ce sun gano akwai maƙarƙashiya da ka iya haifar da tarzoma a lokacin zanga-zangar, yana mai cewa mutane da dama na goyon bayan yin zanga-zangar ne bisa ga jahilci.

Edwerd Buba, ya gargaɗi al’umma da su guji dukkan nau’ukan tarzoma da ka iya faruwa a lokacin gudanar da zanga-zangar inda ya yi nuni da cewa waɗanda su ka shirya ta, suna so su maimaita irin wacce ta faru a ƙasar Kenya inda aka samu tashin-tashina daga zanga-zangar lumana.

Ya ƙara da cewa, duk da cewa ƴan ƙasa suna da damar bayyana kokensu, rundunar soji ba za ta amince da kowace irin tarzoma ba.

Haka nan a gefe guda, rundunar ‘Yan sanda ta gargaɗi al’umma game da tada tarzoma.

Har’ilayau, Shugaba Bola Ahmed Tinubu da gwamnoni da jam’iyyar APC sun rarrashi ƴan Nijeriya da su dakata da gudanar da zanga-zangar.

By Babaji