Zargin ƙirƙirar hukumar bogi: Gwamnatin Tinubu na yunƙurin kare Gbajabiamila – Atiku

Spread the love

Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja 

Tsohon Mataimakin Shugaban ƙasa, Atiku Abubakar, ya ce ƙoƙarin da Fadar Shugaban ƙasa ta yi na kare Shugaban Ma’aikatanta, Femi Gbajabiamila, daga zarge-zargen da ake yi masa ya ƙara jefa gwamnatin Shugaba Bola Tinubu cikin abin kunya.

A cikin wata sanarwa, Atiku ya yi zargin cewa Kasafin Kuɗin 2026 ya ƙunshi tanade-tanaden da suka karkatar da biliyoyin naira zuwa ayyukan gina hanyoyi ta hannun Hukumar Kula da Ilimin Almajirai da Yaran da ba sa zuwa makaranta, duk da cewa ba haka aikin hukumar yake ba.

Ya ce hakan na nuna yadda ake ɓoye ayyuka masu cike da shakku domin karkatar da kuɗaɗen jama’a, yana mai tambayar dalilin da ya sa aka bai wa hukumar ilimi aikin gina hanyoyi.

Atiku ya kuma buƙaci a gudanar da cikakken bincike kan zarge-zargen da ake yi wa Gbajabiamila da suka shafi badakalar Presidential Foreign Interɓention Promotion Council (PFIPC), yana cewa musanta zarge-zargen kawai ba zai wadatar ba.

Haka kuma, ya yi kira ga Majalisar Dokoki ta ƙasa da ta binciki yadda irin waɗannan tanade-tanaden kasafi suka samu amincewa, yana mai cewa ‘yan Nijeriya sun cancanci a bayyana musu gaskiya.

By ukarofi

Leave a Reply