Zargin cin hanci: Jami’an KAROTA sun miƙa shugabansu ga hukumar ICPC

Daga MAHDI M. MUHAMMAD

Hukumar yaƙi da cin hanci da rashawa mai zaman kanta (ICPC) ta fara gudanar da bincike kan zarge-zargen da ake yi wa Baffa Baba Ɗan’agundi, Shugaban Hukumar Kula da abeben hawa ta Jihar Kano (KAROTA).

Hakan ya biyo bayan wata koke da wasu jami’an hukumar KAROTA suka rubuta wa hukumar ICPC inda suke tuhumar shugaban nasu da yawan karbar cin hanci.

A cikin karar da suka shigar mai take: ‘Wasiƙar koka da Shugaban Hukumar Kula da ababen hawa ta Jihar Kano (KAROTA) kan ayyukan cin hanci da rashawa,’ jami’an sun yi zargin cewa tun lokacin da ya hau muƙamin shugaban hukumar a shekarar 2019, ya ke ba da izinin bayar da takardun bogi a duk ofisoshin shiyya.

Sun ce zargin bayar da rasit ɗin na bogi yana gudana ne kawai a hedikwatar hukumar amma ba a kotun tafi da gidanka ba inda ma’aikatan kuɗeɗen shiga na hukumar tara haraji ta Jihar Kano (KIRS) ke karɓar tara.

A cewar koken, Shugaban yana aiwatar da hakan ne ta hannun wani mutum mai suna Shehu, wanda suka ce ya kasance ɗan uwa ne gare shi ba jami’in gwamnatin Jihar Kano ba.