Zargin juyin mulki: Rundunar soji ta miƙa wa Tinubu rahoton bincike

Spread the love

Daga BELLO A. BABAJI a Abuja

Rundunar Sojoji ta miƙa wa Shugaba Bola Tinubu rahoton binciken da ta gudanar akan wasu jami’anta da aka zarga da yi wa gwamnatinsa yunƙurin juyin mulki.

Hukumar Leƙen Asiri ta rundunar (DIA) ta miƙa rahoton ne wata biyu bayan tsare wasu hafsoshin soji 16, da ake zargi da yunƙurin juyin mulkin ciki har da wani mai muƙamin Birgediya Janar.

Wasu manyan hafsoshin soji masu kusanci da binciken sun shaida wa manema labarai cewa, sakamakon binciken ya samu sojojin da ake zargi da laifin yunƙurin kifar da gwamnati, kamar yadda aka tuhume su.

A cewarsu, duk hukuncin da Tinubu ya yanke akan sakamakon binciken, da shi za a ɗauki mataki na gaba.

Majiyar ta ƙara da cewa: “Abin da kawai zan ce shi ne, an samu waɗanda ake zargin da laifi kuma za a hukunta su daidai da yadda doka ta tanada da zarar shugaban ƙasa ya bayar da umarni.”

Ta ƙara da cewa, rahoton ya gano cewa mai muƙamin Birgediya-Janar ɗin da aka tsare, ya samu labarin yunƙurin juyin mulkin, amma bai kai rahoto ga mahukunta ba.

Sun bayyana cewa, umarnin shugaban ƙasa akan rahoton shi ne zai zama jigon duk matakin da rundunar za ta ɗauka akan sojojin, waɗanda a halin yanzu suke tsare a hannun DIA.

By Babaji