
Daga BELLO A. BABAJI
Ƙungiyar Gidauniyar taimako ta mabiya Shi’a dake Jihar Kaduna, wato Ja’afar Addayyar Humanitarian and Charity Foundation, ta barranta daga kalaman kira ga tarzoma da aka jingina su ga Malama Zeenat Zakzaky.
A ranar Asabar ne ƙungiyar ta fitar da wata takarda da ke ɗauke da sanya hannun Shugabanta kuma Babban Limami, Sheikh Abu Ahmad Bin Sa’id, inda ta ce kalaman malamar abin bijirewa ne tare da yin watsi da su ga dukkan mabiya Shi’a a Nijeriya, musamman ga ƙungiyarsu, wadda a tsawon shekaru tana martaba zaman lafiya da haɗin kai.
Ta kuma ce, suna alla-wadai da duk wani nau’i na danniya ko rikici ko kuma ta’addanci.
A yayin taron Mu’tamar da aka gudanar a ranar 11 ga watan Afrilu a Kano, Malamar ta yi wasu kalamai na tunzura mabiya sakamakon kisan wasu mabiyansu a Zaria.
Ƙungiyar ta yi kira ga hukumomin da lamarin ya shafa da su shirya tattaunawa da shugabancin Shi’a ta IMN, wato ‘Islamic Movement in Nigeria’ don samar da mafita ta dindindin game da aukuwar rikici tsakanin mabiyansu da jami’an tsaro yayin gudanar da gangami a Nijeriya.
Kazalika, shugaban ƙungiyar ya bayyana manufofinsu, waɗanda suka haɗa da ƙoƙarin kira ga zaman lafiya a yayin zama da mutane daga mabanbanta aƙidu da addinai a ƙarƙarshin karantarwar Ahlulbaiti (A.S).
