Cin zarafi: Jami’a a Legas ta sallami wasu lakcarori

Spread the love

Daga BELLO A. BABAJI

Hukumar Gudanarwar ta Jami’ar Kimiyya da Fasaha (LASUSTECH) dake Jihar Legas ta sallami wasu lakcarori uku bisa laifin cin zarafi.

Lakcarorin sune Nurudeen Hassan daga Tsangayar Nazarin Aikin Jarida da kuma Kareem Arigbabu da Olayinka Uthman daga Tsangayar Nazarin Fasahar Ƙawa.

Lamarin ya biyo bayan zurfin bincike da aka gudanar akan su gami da cimma matsaya da majalisar shugabancin Jami’ar suka yi a ƙarƙashin kundin dokar kula da lamuran manyan ma’aikatan jami’ar sashe na 5.5.2(v).

Haka kuma, Jami’ar ta jaddada ƙudirinta na cigaba da ƙin lamuntar cin zarafi da kuma jajircewa akan tabbatuwar yanayin karatu mai aminci acikinta.

By Babaji