Zimbabwe: Ɗalibai 106 sun kamu da cutar korona cikin sa’o’i 24

Daga BASHIR ISAH

Rahotanni daga ƙasar Zimbabwe sun nuna ya zuwa ranar Alhamis da ta gabata, an samu ɗalibai 106 daga wasu makarantun ƙasar guda biyu da suka harbu da cutar korona a cikin yini guda.

Sakamakon gwajin da aka yi ya nuna cewa ɗalibai 51 sun kamu da cutar daga makarantar Sacred Heart Girls
High School da ke Esigodini, sannan ɗalibai 55 daga makarantar Umzingwane High School.

Kawo yanzu, ƙasar mai yawan al’ummar da ya haura milyan 15, mutum 1,525 aka tabbatar cutar korona ta yi ajalinsu.

Sai dai a daidai lokacin da aka sake buɗe makarantun ƙasar, tsoron cewa hukumomi ba su shirya ma hakan ba sai ƙaruwa yake.

Ƙwararru a fannin kiwon lafiyar ƙasar sun yi gargaɗin yiwuwa sake ɓullar annobar karo na uku wanda a cewarsu ita ce ta fi haɗari. Tare da cewa muddin ba a ɗauki ingantattun matakan daƙile annobar ba, abin da aka gani yanzu somin taɓi ne kawai.

A cewar gwamnatin ƙasar, ta karɓi allurar rgakafin annobar har guda
1,635,000 amma mutum 123,000 aka samu yi wa allurar tun a tsakiyar Fabrairun da ya gabata.