zamfara: ‘Yan sanda sun daƙile yunƙurin harin ‘yan bindiga

Daga WAKILINMU

‘Yan sanda a jihar Zamfara sun daƙile yunƙurin harin ‘yan ta’adda a ƙauyen Yarkala a gundumar Rawayya da ke cikin ƙaramar hukumar Bunguɗu a jihar.

Mai magana da yawun rundunar ‘yan sandan jihar, SP Muhammad Shehu ne ya bayyana haka ranar Asabar a Gusau, babban birnin jihar.

A cewar jami’in, jami’ansu sun sunkuya aiki ne bayan da suka samu labarin shirin da ‘yan bindigar suka yi don kai hari a ƙauyen Yarkala a Alhamis da ta gabata.

“Bayan da muka samu kira, ba a yi wata-wata ba sai jami’anmu suka dira a yankin inda suka daƙile shirin ‘yan bindigar lamarin da ya sa suka tsere cikin daji don neman mafaka.”

Ya ce kayayyakin da aka ƙwace daga wajen ‘yan bindigar sun haɗa da bidiga ƙirar AK 47 mai lamba 1983NI2328 da kuma alburusai da dama.

A wata sabuwa, a Juma’ar da ta gabata sai da rundunar ‘yan sandan tare da haɗin gwiwar Ma’aikatar Tsaro da Harkokin Cikin Gida suka kuɓutar da wasu mutum 11 daga hannun ‘yan fashi waɗanda aka yi garkuwa da su a dajin da ke kusa da Gobirawan Chali a ƙaramar hukumar Maru.

10 daga cikin waɗanda aka kuɓutar ɗin ‘yan asalin Kyakyaka da Tungar Haki da kuma ƙauyen Gidan Ango ne da ke ƙaramar hukumar Gusau, yayin da gudan ya kasance ɗan jihar Kaduna.

Shehu ya bayyana kuɓutar da waɗanda lamarin ya shafa a matsayin tasirin shirin wanzar da zaman lafiya a jihar na Gwamna Mohammed Bello Matawalle.

Ya ce an miƙa waɗanda aka ceto ɗin ga Kwamishinan Tsaro da Harkokin Cikin Gida inda daga bisani za a sada su da ahalinsu.

Ya ƙarasa da cewa, tuni sun soma gudanar da bincike kan batun garkuwa da aka yi da waɗanda aka kuɓutar kuma bayan kammalawa za su bayyanar da sakamakon binciken nasu ga al’umma.