Zuri’ar Babandede da masoyansu sun yaba wa Sarkin Haɗeja kan naɗa Magajin Rafin Haɗeja

Spread the love

Daga MUHAMMAD MUJITABA a Kano

Zuri’ar Babandede a masarautar Haɗeja sun yaba wa Maimartaba Sarkin Haɗeja, Alhaji Adamu Abubakar Maje Haɗeja kan naɗa Alhaji Muhammad a matsayin Magajin Rafin Masarautar Haɗeja.

Hajiya Amina Muhammad Babandede ita ce babbar yaya ga Magajin Rafin Haɗeja, Muhammad Babandede, sai kuma Muhammad Babandede wanda shi ne tsohon shugaban hukumar lura da shige da fice na Nijeriya da sauran ‘yan uwa da masoya sun nuna godiya ga Allah Maɗaukakin Sarki kan ƙarrama su da Maimartaba Sarkin Haɗeja Alhaji Adamu Abubakar Maje ya yi musu da naɗa ɗan uwansu a wannan sarauta mai tasiri da kwarjini a masarautar Haɗeja da ma jihar Jigawa da Nijeriya bakiɗaya.

Hajiya Amina ta bayyana cewa Maimartaba Sarkin Haɗeja mutum ne mai alƙawari da karrama al’umma domin ya karrama kuma ɗan uwansu ya gaji wannan gida saboda haka tsakaninsu da masarautar Haɗeja sai addu’ar alkairi da fatan zaman lafiya da kwanciyar hankali a masarautar da ma jihar Jigawa bakiɗaya.

Haka ita ma Hajiya Amina Aliyu Babandede, mai ɗakin Magajin Rafin Haɗeja, ta bayyana cewa su kam ba wani abu da za su ce akan wannan sarauta sai dai su ce Allah ya saka da alkairi ga Maimartaba Sarkin Haɗeja da addu’a kan Allah ya yi wa Magajin Rafin Haɗeja domin mutum ne wanda ba zai kunyata masarautar Haɗeja musamman ganin yadda wannan sarauta ta samu karɓuwa da ɗaukaka a masarautar Haɗeja da ma Jigawa baki ɗaya.

Saboda haka ta yaba wa ɗaukacin baƙin da suka halarci taron wannan gagarumin naɗi waɗanda suka zo daga saƙo da lungu na Njieriya da wajenta domin shaida muhimmiyar ranar.

A ƙarshe shi ma Manajan darakta na kamfanin takin zamani Alhaji Miko Maidubu ya ce shi da shugaban kamfanin takin zamani na ƙasa Alhaji Ali Mai Taki suka yi takakkiya daga Kano wajen taya Magajin Rafi murna da addu’a kan wannan sarauta da Allah ya ba shi wanda Maimartaba Sarkin Haɗeja ya naɗa shi.

Taron dai ya samu mahalarta daga ko’ina inda kuma suka bayyana gamsuwarsu da wannan naɗi na Magajin Rafin Haɗeja irin su Uba Bawan Allah Taura, Usman Indayako mazaunin Legas da shugaban ƙungiyar Miyetti Allah na ƙaramar Guri Alhaji Musa Bala Guri, da sauransu duk sun yi fatan alkairi da gamawa lafiya ga Magajin Rafin Haɗeja.

By ukarofi