
Daga BELLO A. BABAJI a Abuja
Kungiyar kare Haƙƙin Ɗan-adam ta Ƙasa da Ƙasa, International Human Rights Commission – Relief Fund Trust (IHRC-RFT) a Nijeriya, ta nuna matukar alhini, damuwa da Allah-wadai kan mummunan kisan gillar da aka yi wa Malama Ummulkhairi a Mararaban Jos, Karamar Hukumar Igabi, Jihar Kaduna, bayan wasu mutane sun zarge ta da wani laifi ba tare da gabatar da ita gaban hukuma ko kotu ba.
A wata sanar da Daraktanta na Nijeriya, Amb. Abdullahi Bakoji Adamu ya fitar a ranar Laraba, IHRC-RFT ta ce wannan lamari abin takaici ne matuka kuma ya saba wa dukkan ka’idojin adalci, mutunta rayuwar dan Adam da kuma tsarin mulkin dimokuradiyya. A matsayinta na kungiya mai rajin kare hakkin bil’adama, IHRC-RFT Nigeria tana jaddada cewa babu wani mutum ko taron jama’a da ke da ikon yanke hukunci ko aiwatar da hukunci kan wani dan kasa ba tare da bin hanyoyin da doka ta tanada ba.
A cewarta, haƙƙin rayuwa yana daga cikin muhimman hakkokin dan Adam da Kundin Tsarin Mulkin Tarayyar Najeriya da dokokin kasa da kasa suka tabbatar. Sashe na 33(1) na Kundin Tsarin Mulkin Tarayyar Najeriya na shekarar 1999 (kamar yadda aka yi masa gyara) ya tabbatar da cewa kowane mutum yana da hakkin rayuwa, kuma ba za a hana shi rayuwarsa ba sai daidai da hukuncin kotu bayan an same shi da laifi bisa tanadin doka.
Haka kuma, ta ce sashe na 34(1) na Kundin Tsarin Mulkin Nijeriya ya tabbatar da hakkin mutunci tare da haramta duk wani nau’i na cin zarafi, azabtarwa ko wulakanta dan Adam. Kona mutum da rai ko kashe shi ta hanyar taron jama’a babban take hakki ne ga wannan tanadi na kundin tsarin mulki.
Bugu da ƙari, Sashe na 36(1) na Kundin Tsarin Mulkin Najeriya ya tabbatar da hakkin samun shari’a cikin adalci, yayin da Article 10 na Universal Declaration of Human Rights (UDHR) ya tabbatar da cewa kowane mutum yana da hakkin a saurare shi cikin gaskiya da adalci a gaban kotu mai zaman kanta kafin a yanke masa hukunci.
Har ila yau, ƙungiyar ta ƙara da cewa “Article 3 na Universal Declaration of Human Rights ya bayyana cewa: “Everyone has the right to life, liberty and security of person.” Ma’ana, kowane mutum yana da hakkin rayuwa, ‘yanci da kariya ga lafiyarsa.”
Saboda haka, ko da mutum yana fuskantar zargi, wannan kaɗai ba ya cire masa hakkinsa na samun kariyar doka da kuma shari’a ta gaskiya. A karkashin tsarin mulkin doka, kotu ce kadai ke da ikon tantance laifi da yanke hukunci, ba taron jama’a ba.
IHRC-RFT Nijeriya tana nuna matukar damuwa kan yadda zargi, jita-jita ko hasashe ke ci gaba da zama sanadin rasa rayukan bayin Allah a wasu sassan kasar nan. Wannan dabi’a ta daukar doka a hannu babbar barazana ce ga zaman lafiya, tsaro da hadin kan al’umma.
Muna maraba da matakin da hukumomin tsaro suka dauka na kama wasu da ake zargi da hannu a wannan mummunan laifi. Sai dai muna kira ga rundunar ‘yan sanda da sauran hukumomin tsaro da su gudanar da cikakken bincike mai zurfi, adalci da gaskiya domin gano duk wanda ya shirya, ya aiwatar ko ya taimaka wajen aikata wannan aika-aika.
Muna kuma kira ga hukumomin shari’a da su tabbatar da gurfanar da duk wadanda bincike ya tabbatar suna da hannu a wannan kisan gilla domin su fuskanci hukuncin da doka ta tanada. Dole ne a tabbatar da cewa an yi adalci ba tare da la’akari da matsayin mutum, addininsa, kabilarsa ko wata alaka ba.
IHRC-RFT Nigeria za ta ci gaba da sanya ido kan yadda binciken wannan lamari ke gudana tare da bibiyar matakan da hukumomi ke dauka domin tabbatar da cewa an yi cikakken adalci ga marigayiya Malama Ummulkhairi da iyalanta.
Muna kira ga shugabannin addinai, sarakuna, kungiyoyin farar hula, kafafen yada labarai da daukacin al’umma da su kara wayar da kan jama’a game da muhimmancin mutunta doka, kare hakkin bil’adama da kuma gujewa yanke hukunci bisa jita-jita, hasashe ko zargi.
Adalci ga Malama Ummulkhairi ba hakkin iyalanta kadai ba ne, hakkin al’umma baki daya ne. Rashin hukunta masu hannu a irin wannan danyen aiki na iya kara karfafa masu daukar doka a hannu da kuma jefa zaman lafiyar al’umma cikin hadari.
Muna mika ta’aziyyarmu ga iyalan marigayiyar, ‘yan uwanta da daukacin al’ummar da wannan mummunan lamari ya shafa. Muna addu’ar Allah Madaukakin Sarki Ya jikanta da rahama, Ya gafarta mata kura-kuranta, Ya sanya Aljannatul Firdausi ta zama makomarta, Ya kuma bai wa iyalanta hakurin jure wannan babban rashi.
An fitar da wannan sanarwa ne domin kare martabar ɗan-adam, tabbatar da bin doka da kuma neman cikakken adalci ga Malama Ummulkhairi, kamar yadda ƙungiyar ta bayyana.
