An rantsar da sababbin sanatocin da aka zaɓa a zaɓukan cike gurbi

Spread the love

Daga BELLO A. BABAJI a Abuja

A yau Laraba Majalisar Dattawa ta rantsar da sababbin sanatoci guda huɗu da suka yi nasara a zaɓukan cike gurbi da Hukumar Zaɓe(INEC) ta gudanar a ranar Asabar da ta gabata.

An gudanar da rantsarwar ne ƙarƙashin jagorancin Shugaban majalisar Godswill Akpabio a zaman majalisar a Abuja, inda sabbin sanatocin suka fara wakiltar mazaɓunsu a hukumance bayan karbar takardun shaidar cin zabe daga INEC.

Sabbin sanatocin sune Dayo Faduyile mai wakiltar Ondo ta Kudu, Envulu Anza mai wakiltar Nasarawa ta Arewa, Ikeje Asogwu mai wakiltar Enugu ta Arewa, da kuma Olaka Nwogu, Ribas ta Kudu maso Gabas.

Kujerun sanatocin guda uku sun kasance babu kowa ne sakamakon rasuwar waɗanda suka rike su a baya, yayin da kujerar Ondo ta Kudu ta zama babu kowa bayan nadin tsohon sanatan yankin, Jimoh Ibrahim, a matsayin wakilin Njjeriya na dindindin a Majalisar Ɗinkin Duniya.

A jawabinsa, Sanata Akpabio ya yi kira a gare su da su fifita muradun kasa fiye da na jam’iyyunsu, yana mai jaddada cewa yanzu suna wakiltar Nijeriya ne ɗungurungum.

Haka kuma ya shawarce su da su yi nazari kan Kundin Tsarin Mulkin 1999 da dokokin majalisar domin gudanar da aikinsu yadda ya dace.

By Babaji

Leave a Reply