Daga JOHN D. WADA a Lafiya
Ɗakin karatu na musamman na ƙasa wato National Library of Nigeria a turance reshen Jihar Nasarawa dake birnin Lafia fadar gwamnatin jihar ya koka kan rashin wutar lantarki a cibiyar yana mai cewa cibiyar ta yi ta aiki ba tare da wutar lantarki ba har na tsawon shekaru sama da 14.
Shugabar reshen Mrs. Angela Anya ce ta bayyana hakan a wata hira na musamman da tayi da wakilin Manhaja a jihar a Lafia a mako da ake ciki.
Anya tace duk da wutar lantarki na da matukar muhimmanci ga bincike da koyo da adana bayanai a cibiyar amma dogon lokacin da aka ɗauka ba tare da wuta ba ya kawo cikas ga ayyukan karatun da sauran hidimomin cibiyar baki ɗaya.
A cewarta baya ga rashin wutar lantarkin ɗakin karatun na kuma fuskantar wasu ƙalubale ciki har da rashin haɗin Intanet da rashin isassun ɗakunan ajiye littattafai.
Saboda haka sai tayi amfani da damar inda ta yi kira ga gwamnatin jihar Nasarawa da kamfanoni da ɗaiɗaikun mutane masu kishin ƙasa da su tallafa wa cibiyar domin ya iya sauke nauyin da doka ta ɗora masa yadda ya kamata.
Ta bayyana cibiyar ilimi irin wannan na ƙasa a matsayin ma’ajiyar tarihin al’adu da tarihi na ƙasa inda ta kuma shawarci masu bincike da masu kirkire-kirkire da malamai da su yi amfani da albarkatunsa.
Ta kuma shawarci marubuta da masu bincike da su ajiye kwafin wallafe-wallafensu da sakamakon bincikensu a ɗakin karatun domin adanawa a cikin tarihin ƙasa wato abinda ake kira National Bibliography kenan.
Anya ta kuma yi kira ga kamfanoni masu zaman kansu da masu taimako da su tallafa wa ƙoƙarin gwamnati ta hanyar saka jari a cibiyar ta zamani tare da sanya musu albarkatun dijital da bayanan bincike da taskokin da aka sarrafa su ta dijital domin adana tarihin ƙasa.
Har ila yau ta kuma bukaci ‘yan ƙasa musamman ɗalibai su riƙa ziyartar cibiyar don bincike da ƙirƙire-ƙirƙire da cigaban fasaha da sauran su.
Da take magana kan rajistar lambar littattafai ta duniya (ISBN), Anya ta gargaɗi mawallafa su guji buga kayan ilimi da al’adu ba tare da samun lambobin da suka dace ba inda ta lura cewa irin wannan aiki laifi ne kuma yana jawo hukunci mai tsanani a ƙarƙashin doka.
