Ɗan majalisar dokokin Bauchi, Muhammad Wanzam ya rasu

Spread the love

Daga BELLO A. BABAJI a Abuja

Ɗan majalisa mai wakiltar mazaɓar Sakwa a Majalisar Dokokin Jihar Bauchi, Hon. Mohammed Wanzam ya rasu a safiyar ranar Lahadi.

Har zuwa lokacin rasuwarsa, Hon. Wanzam shi ne shugaban kwamitin kasafi na majalisar.

Kakakin majalisar, Rt. Hon. Abubakar Y. Sulaiman ne ya sanar da rasuwar marigayin a wata sanarwa.

Mai magana da yawun kakakin, Mukhtar Garba Kobi a sanarwar, ya bayyana marigayin a matsayin jajirtaccen ma’aikatacin gwamnati da ya hidimta wa mazaɓarsa da jihar daidai gwargwado.

An gudanar da jana’izar marigayin ne a Masallacin Juma’a na Gwallaga da ke garin Bauchi da misalin ƙarfe 11 na safe.

Ya kuma yi masa addu’ar Allah ya jiƙan sa ya kuma gafarta masa kurakuransa tare da karɓar ayyukansa kyawawa.

By Babaji

Leave a Reply