Daga UMAR GARBA a Katsina
Tun da farko an kai ɗan wasan Katsina United, Chinedu Ozor, sashen kula da marasa lafiya na gaggawa na babbar asibitin Katsina bayan da aka sanar da mutuwarsa a jiya Talata, bayan ɗan wasan ya faɗi a yayin da yake taka wasan share fagen shiga kakar wasa ta firimiyar Najeriya (NPFL) a ranar Talata.
Rahotanni sun ce Ozor ya ya yanke jiki ya fadi ne a lokacin wasan Katsina United da Niger Tornadoes, inda nan da nan aka garzaya da shi asibiti da ke kusa, sai dai likita ya tabbatar da mutuwarsa tun a lokacin.
Bayan da ƙungiyar ta kai gawarsa Babban Asibitin Katsina, an ruwaito cewa ma’aikatan lafiya dake a ‘mortuary’ sun lura da motsinsa, lamarin da yasa aka ɗauke shi aka mayar da shi sashin kula da marasa lafiya na gaggawa.
Jami’in watsa labarai na ƙungiyar Katsina United, Nasir Gixe ya tabbatar da faruwar lamarin inda ya ce, “Lokacin da muka kai shi asibiti da ke kusa, likita ya tabbatar da mutuwarsa. Mun tattara rahoton ‘yan sanda muka mayar da shi Babban Asibitin Katsina inda aka ce shi ma ya mutu. Sun kai gawarsa asibiti da ke can,” in ji Giɗe.
“Daga baya, ma’aikatan lafiya sun sanar da mu cewa an mayar da shi asibiti daga ɗakin ajiye gawa lokacin da suka lura da sauran motsi a jikinsa.”
Wannan lamari ya faru ne bayan da Katsina United ta sanar da mutuwar Ozor tun da farko, wanda hakan ya sa aka fara aike wa da saƙonnin ta’aziyya daga tsohuwar ƙungiyarsa ta Kano Pillars da sauran ƙungiyoyi.
