Ƙarin kashi 50: Gwamnoni har yanzu ba mu gani a ƙasa ba

Spread the love

Daga Mamman Danbala

Ko da za ka yi zagi ne, ka fara karantawa, don sanin yadda aka yi da arzikin ƙasarka a sanda ka ke kokawa da tsananin rayuwa.

Bahaushe na yin wata karin magana da ke cewa, ”Babba Juji”. Wannan na daga dalilin da ya sa duk lokacin da muka tashi neman haƙƙoƙinmu, sai mu ɗunguma zuwa ga Gwamnatin Tarayya, mu mance da gwamnonin jihohi, waɗanda muke da haƙƙoƙi masu tarin yawa a kansu. 

Tun bayan hawan Tinubu mulki a ƙasar nan ake aiko da kuɗaɗe daga Gwamnatin Tarayya zuwa gwamnonin jihohi da kuma ƙananan hukumomin ƙasar nan 774, kuɗaɗen na samuwa ne daga haraji (Reɓenue) da Gwamnatin Tarayya ke samu a kowanne wata, ta kuma raba shi tsakanin matakan gwamnati uku; ta tarayya, jiha da kuma ƙaramar hukuma. 

Daga alƙaluman da FAAC ta fitar, jihohi da dama sun samu ƙarin kaso 50 cikin 100 na abinda suke karɓa a kowane wata idan aka kwatanta da gwamnatin da ta gabata. Wasu jihohin kuma sun samu ƙarin kaso 40 cikin 100.

A watanni biyar  na farkon shekarar 2024, (Janairu zuwa Mayu), Gwamnatin Tarayya, gwamnatin jihohi 36 da kuma ƙananan hukumomin 774 sun raba kuɗi fa ya kai tiriliyan 10.13 a tsakaninsu. 

Rahoton ya nuna cewa, jihohin da suka samu ƙarin kaso 50 cikin 100 na abinda suke samu a baya sun haɗa da; Abiya, Benuwe, Ekiti, Katsina, Kwara, Legas, Ogun, Osun, Filato da kuma Taraba.

Ragowar jihohin Adamawa, Anambra, Borno, Kuros Ribas, Ibonyi, Inugu, Kano, Kebbi, Nasarawa, Neja, Oyo, da Sokoto sun samu ƙarin kaso 40 cikin 100.

Wani arashi da aka samu shine, kason da gwamnatin jiha ta samu a shekarar farko ta Tinubu ya ƙaru da kashi 53.8 cikin 100 idan aka kwatanta da abinda suke samu a gwamnatin da ta shuɗe, wanda ya kai Naira triliyan 4.54, adadin da ya kusan ninkawa sau biyu idan aka kwatanta da Naira Tiriliyan 2.95 da aka raba musu a zamanin mulkin Buhari.

Haka zalika kuɗaɗen shiga da aka raba wa ƙananan hukumomi a ƙarƙashin Gwamnatin Tinubu ya ƙaru da kashi 76 cikin 100, wanda aka samu karin Naira Tiriliyan 1.38. A yanzu ƙananan hukumomi na karɓar Naira Tiriliyan 3.84 saɓanin Naira tiriliyan 2.18 da Gwamnatin Buhari ta raba musu a baya. 

Tambayoyinmu a nan su ne;

1. Me ya hana gwamnonin jihohi yin abinda ya kamata da kuɗaɗen nan musamman yanzu da ake fama da ƙalubalen tashin farashin kayayyakin abinci da kuma karancin kuɗi a hannun mutane ta kan zuba jari a ɓangaren noma, kiwo da kuma hada-hadar kasuwanci? 

2. Me ya sa gwamnonin jihohi ba su yi amfani da wani kaso wajen raya al’umma bayar da samar da sabbin hanyoyin da za su wadata jihohin su da abinci tare da samar wa matasa ayyukan yi da za su shagalar da su ga barin ɓarna? 

3. Me ya sa ba za su ware wani adadi na kuɗi ba akan noma don haɓaka yawaitar abinci da samar da aiki ga matasa, duk da cewa Gwamnatin Tarayya ta aiko musu da takin zamani da sauran kayan noma na zamani?

4. Me ya sa gwamnoni ba su ƙirƙiro sabbin hanyoyin dogaro da kai tare da bayar da jari ga al’ummar jihar, don su ɗan rage yawan talauci tsakanin al’umma ba?

Haƙƙi ne na dukkan ɗan ƙasa ya san me akai da dukiyarsa, ina aka zuba su, ya akai aka kashe su, musamman in babu abin nunawa a ƙasa. Mun ga Jihar Kano ta kashe kimanin Naira biliyan 34 da ɗoriya a gudanarwar harkokin yau da kullum (recurrent eɗpenditure) cikin watanni ukun farkon wannan shekara ta 2024, amma ba ta kashe makamancin haka a ɓangaren noma ko samar da hanyoyin dogaro da kai ba, don haɓaka tattalin arzikin Jihar Kano. Mun ga jihohin da suka kashe kimanin Biliyan 10 akan ciye-ciye da shaye-shayen lemuka da kayan maƙulashe. Wannan duka na faruwa ne a lokacin da al’umma ke kokawa kan abinda za su ci da iyalansu. 

Mu na buƙatar bayani!

Ɗanbala ya rubuto ne daga Abuja

By ukarofi