Ƙasar da ke haifar da tashin hankali a duniya

Spread the love

Daga LUBABATU LEI

Wani nazarin da cibiyar nazari ta Cato ta ruwaito a watan Afrilun bana ya yi nuni da cewa, cikin shekaru biyun da suka gabata, a ƙalla jami’an soja da suka samu horo daga Amurka sun tsara juyin mulki har sau huɗu, daya a shekarar da muke ciki a ƙasar Burkina Faso, daya a bara a ƙasar Guinea, sauran biyun kuma a ƙasar Mali.

Baya ga haka, ƙididdigar da aka fitar ta yi nuni da cewa, daga farkon ƙarni na 20, Amurka ta kuma tsara gomman juye-juyen mulki a ƙasashen Latin Amurka.

Haƙiƙa, yadda Amurka ta sha kitsa juyin mulki ko kuma ƙaddamar da yaƙi kan wata ƙasa kai tsaye ko a fakaice, a yunƙurin haifar da rikici a wata ƙasa da ma cimma burin juyin mulkinta, ba ɓoyayyen abu ba ne.

A kwanaki baya, tsohon babban jami’in Amurka wanda ta taba zama mai taimaka wa shugaban kasar kan harkokin tsaro, John Bolton ya amince cewa, ya taba “taimakawa wajen tsara juyin mulki a wasu ƙasashe”, abin da ya girgiza al’ummar ƙasa da ƙasa.

Hakan ya nuna halin ƙasar ta Amurka na nuna fin ƙarfi a duniya, wato tana tsoma baki a harkokin cikin gidan sauran ƙasashe yadda ta ga dama ba tare da yin la’akari da dokokin ƙasa da ƙasa ba, kuma ta kan kifar da duk wata gwamnati da ba ta yi mata biyayya, kawai sabo da fi ƙarfi.

Mu kalli yanayin da ake ciki a ƙasashen Libya da Syria da Iraki da Afghanistan……za mu ga irin barnar da Amurka ta haifar musu domin cimma buri da moriyarta, duk da cewa tana wa kanta kirarin mai kare ‘yanci da dimokuradiyya, amma kowa ya ga abin da ta aika a zahiri.

Lallai ta cika mai haifar da tashin hankali a duniya.

Mai Zane: Mustapha Bulama

By Editor