Ribar masana’antun Sin ta ƙaru da kaso ɗaya bisa ɗari a rabin farko na bana

Daga CMG HAUSA

Ribar manyan masana’antun ƙasar Sin ta ƙaru da kaso ɗaya bisa ɗari a rabin farko na shekarar bana, kamar yadda alƙaluman kididdiga da aka fitar a yau Laraba suka tabbatar da hakan.

Babban jami’i a hukumar ƙididdigar ƙasar NBS Zhu Hong, ya alaƙanta wannan ci gaba, da matakan aiwatar da cikakkun tsarukan shawo kan annobar COVID-19, da na raya tattalin arziki da ci gaban al’umma, da kuma matakai daban daban da aka aiwatar, domin saita akalar tattalin arzikin ƙasar.

Mai fassarawa: Saminu Alhassan daga CMG Hausa