Ƙasashen Afirka suna da hikimar zaɓen abokan haɗin gwiwa da kansu

Daga CMG HAUSA

Kakakin ma’aikatar harkokin wajen ƙasar Sin Zhao Lijian ya bayyana a gun taron manema labaru da aka gudanar a yau cewa, Afirka ita ce Afirka ta jama’ar Afirka, kuma ƙasashen Afirka tana da hikima da sanin ya kamata wajen zaɓen abokan haɗin gwiwarta.

Nuna goyon baya ga bunƙasuwar Afirka, alhaki ne da ƙasa da ƙasa suka ɗauka tare.

Rahotanni sun bayyana cewa, kwamandan rundunar sojojin Amurka dake nahiyar Afirka Stephen Townsend ya bayyana a jiya cewa, yanayin tsaro a nahiyar Afirka yana da sarƙaƙiya, Sin da Rasha sun fi yin amfani da hanyoyin diplomasiyya, da tattalin arziki, da na soja, don kara faɗaɗa zuba jari da tasirinsu a nahiyar Afirka, da kuma amfani da taushin hali don neman sabuwar dangantakar abokantaka a nahiyar.

Game da wannan batu, Zhao Lijian ya yi nuni da cewa, jami’an ƙasar Amurka sun nace kan ra’ayin yaƙin cacar baka tsakanin ƙasashe masu tsarin jari-hujja da masu bin tsarin gurguzu, da neman yin takara a tsakanin ƙungiyoyin ƙasa da ƙasa, da sanya ido kan harkokin sauran ƙasashen duniya, da mayar da hankali kan daƙile tasirin wasu ƙasashe a Afirka, ayyukansu ko kaɗan bai dace ba.

Zhao Lijian ya yi nuni da cewa, har kullum ƙasar Sin tana nuna kyakkyawar fata ga bunƙasuwar nahiyar Afirka, kana taimako da goyon bayan da take bai wa Afirka wajen tabbatar da zaman lafiya da samun ci gaba ba zai ragu ba.

Sin tana maraba da ƙasashen duniya ciki har da ƙasar Amurka, da su ƙara maida hankali wajen zuba jari ga nahiyar Afirka, kuma tana fatan dukkan abokan hulɗa, za su ci gaba da tabbatar da samun moriyar juna, da samun nasara tare, da bayar da gudummawar albarkatunsu da lokacinsu da ƙarfinsu wajen biyan bukatun Afirka na samun ci gaba, da yin ayyukan alheri masu amfani, wadanda za su kai ga samar da haɗin gwiwa mai inganci, ta yadda za a samu zaman lafiya da bunƙasuwa a Afirka.

Fassarawar Zainab