Duk lokacin da na fitar da sabon littafi na kan kashe wayata na ɗan lokaci – Zainab Birget

Spread the love

“Ba zan bar rubutu ba har sai idan shine ya bar ni”
Daga MUkHTAR YAkUBU a Kano

Zainab Lawan Birget tana ɗaya daga cikin fitattun mata marubuta da suka ɗauki lokaci mai tsawo a cikin harkar, domin kuwa ta shafe sama da shekaru 20 tana yin rubutun wanda kuma a tsawon lokacin da ta shafe ta rubuta littattafai masu yawan gaske. Ganin yadda harkar rubutun ta koma a yanzu a matsayinta ta tsohuwar marubuciya, mu ka nemi jin ta bakinta a game da irin hangen ta a kan makomar rubutu da kuma littattafai a yanzu da kuma nan gaba. Ku biyo mu, ku ji yadda hirar ta kasance:

MANHAJA: Da farko za mu so ki gabatar da kanki ga masu karatunmu.
ZAINAB: To ni dai suna na Zainab Lawan Birget, kuma ni haifaffiyar garin Kano ce, a unguwar Fagge, a nan aka haife ni, kuma na yi makarantar Firamare da sakandare duk a Kano, daga baya aka yi mini aure a unguwar Birget inda mu ke zaune da mijina, kuma Allah ya albarkace mu da yara masu yawa duk maza ne, ɗaya daga cikinsu ce mace, amma a yanzu Allah Ya yi wa maigidana rasuwa, sai ni da yarana mu ke rayuwa. Alhamdulillahi mu na godiya da arzikin yara da Allah Ya yi mana, yadda har mun kai ga aurar da ‘ya mace, kuma ga shi a yanzu mu na cikin rufin asiri.

ko ya aka yi kika samu kanki a cikin harkar rubutu?
To a gaskiya ni tun Ina ƙarama wato lokacin da na ke makarantar firamare tun a nan na samu kaina a cikin son rubutu, saboda ni Ina da son karatu kuma duk abin da na karanta sai na ji Ina son na rubuta shi. To, da haka ne rubutun sai ya zama a jikina, domin ko a cikin ƙawayena sai da ya zama na fita ta daban a wajen rubutu da karatu, kuma da na girma hankali ya zo mini, sai kuma na fahimci shi rubutun hanya ce ta isar da saƙo, kuma ka san duk wani mutum da ka gani to akwai saƙo a zuciyarsa da yake son ya isar da shi ga jama’a, to ni kuma sai na ga ta hanyar rubutu ne kawai zan iya isar da na wa saƙon don haka sai na samu damar shiga harkar rubutun domin na samu na cimma burin isar da saƙon da na ke da shi.

Da wanne salo kika fara yin rubutunki?
To, da yake a lokacin da na shigo harkar duk salon rubutun da a ke yi na soyayya ne, ni kuma sai na ɗauki wani salo na faɗakarwa, amma dai a cikin salon soyayyar, don haka sai na mayar da hankali a kan irin na wa salon, kuma alhamdulillahi, na fara kamar wasa, sai kuma cikin ikon Allah rubutun na wa ya samu karvuwa har ta kai ana karanta wa a gidanjen rediyo, kuma sai littattafan na wa suka ƙara karvuwa kasancewar masu karatun da sauraro a rediyo matasa ne da kuma mata, kuma abubuwan da na ke rubutu a kansu na faɗakarwa sun shafe shi to abin ya ƙara wa rubutun na wa tasiri sosai a cikin jama’a. Domin a rubutuna na kan taɓo matsalar zamantakewar aure musamman abin da ya shafi uwar miji da kuma zaman miji mai mata uku zuwa huɗu, sai kuma matsalar matar uba da ‘ya’yan miji, to su ne matsalolin da na fi mayar da hankali a kansu wajen rubutuna.

Aƙalla kin rubuta Littattafai za su kai nawa?
To da yake na daɗe a cikin harkar, ko ban kira kaina tsohuwar marubuciya ba, to na san na daɗe a harkar kusan shekaru 27 kenan, kuma a tsawon wannan lokacin na rubuta littattafai za su kai 30 waɗanda aka buga, suka shiga kasuwa kenan, amma idan har waɗanda ba a buga ba, to za su fi hakan, amma dai har zuwa wannan lokacin da na ke yin rubutun na ɗauke shi ne a matsayin ra’ayi don ban mayar da shi wata harkar kasuwanci ba, don haka idan lokaci ya samu na yi, kuma lokacin da hidimomi suka yi yawa, sai na ajiye zuwa wani lokacin kuma na sake dawowa, kuma har zuwa wannan lokacin ban tantance lokacin da zan ce ga lokacin da zan tsaya na huta ba, saboda yana daga cikin tsarina, kuma ba na jin akwai wani lokacin da na tsara zan bari duk wani matsayi da na taka. Ba na jin zan iya barin rubutun, amma dai na san akwai lokacin da zai zo ko Ina so ko ba na so zan bari.

ko akwai wani ƙalubale da kika fuskanta a cikin harkar?
To, ƙalubale ba zan iya cewa babu ba, domin duk lokacin da ka yi rubutu kuma ya yaɗu a cikin jama’a, dole ne ba za a rasa matsaloli na nan da can ba, don da dai wani lokacin ba shi da yawa, amma da yake harkar jama’a ce wani lokacin sai ka ga ka samu kanka cikin matsala. Amma dai abin da ya fi zama ƙalubale a wajenmu musamman ma mu da mu ka daɗe mu na harkar ba zai wuce na ‘yan kasuwa ba, domin za ka ga mutum ya kai kaya kasuwa an sayar, amma kuɗin bai dawo ba, kuma sai ka yi ta zuwa babu kaya babu kuɗin kaya. Sai kuma su masu karatun, don su masu karatu ba su san yadda mutum zai yi rubutunsa ba har ya kai ga an wallafa littafi don haka duk lokacin da ka fitar da littafi na ɗaya suna jiran na biyu sai su yi ta jin haushin ba ka fito mu su da na biyu ko na uku ba, sannan idan ka saki littafi musamman wanda ya karɓu, to fa ka rinƙa samun kiran waya a hana ka saƙat, wannan ta sa idan na fitar da littafi sai na kashe waya ta har na tsawon lokaci, duk da cewar wasu za su kira ka ne su yabe ka, amma wasu za su kira ka ne su faɗi maganganu masu zafi.

Wanne irin nasarori kika samu a harkar rubutun?
Alhamdulillahi! Nasarori da aka samu a cikin harkar suna da yawa. Ba zan manta ba a cikin wannan harkar an ba ni kambun karramawa har sau biyu, kuma da yake shi rubutu harka ce ta ilimi domin jahili ba zai iya rubutu ba, don haka a matsayinmu na masu rubutu, duk da dai ba malamai ba ne, amma mun samu nasarar faɗakar da jama’a wanda da dama za su kira mu suna godiya, sannan an samu nasarar ƙulla alaƙa da jama’a wanda ko cikin taron biki idan mu ka shiga za ka ga mutane su kan taso su ganka. kuma ko ba komai wani lokacin za ka samu wani alherin da jama’a za su yi maka a matsayin ki ta marubuciya.

Ya kike ganin harkar rubutu a wannan lokacin?
To duk da dai harkar rubutu a yanzu ta ja baya ba kamar a shekarun da suka gabata ba, yadda mu ka ci gajiyar rubutun sosai, to ni dai a yanzu ba zan iya cewa harkar rubutu ta taɓarɓare ba, domin ni har yanzu rubutun da na yi na littafi ana karanta wa a gidanjen rediyo. Sai dai a ɓangaren kasuwa zan iya cewa harkar rubutu ta rushe, saboda a yanzu kasuwar kusan babu ita, don haka ko mutum ya saka kuɗi ya buga littafin, to ba zai fito ba ballantana a yi maganar riba. Sai dai da yake su marubutan masu tafiya da zamani ne, tun da kasuwar ta koma ‘online’ su ma sai suka juya a ke ɗora wa a YouTube da sauran su. To don haka dai za mu iya cewar harkar rubutun ba ta mutu ba, sai dai kasuwar da mu ka saba kaiwa a baya ita ce a yanzu ta mutu.

A yanzu waɗanne abubuwa ne kike alfahari da su a matsayinki ta marubuciya?
Alhamdulillahi! Akwai abubuwa masu yawa da na ke alfahari da su a matsayina ta marubuciya, abin da na fi alfahari da shi shine, tun da na ke rubutu ban tava samun wata matsala a tsakanina da hukuma ko wasu mutane ba, da a ke ganin na vata mu su ko na yi ba daidai ba, don haka wannan ma kaɗai abin alfahari ne, kuma a matsayina ta uwa ba na son na yi wani abu da zai vata tunani ko tarbiyyar yara ba, don haka a cikin rubutuna na kan yi taka-tsantsa wajen saka kalmomin sakin baki. Don haka Ina godiya ga Allah da ya sa rubutun da na ke yi babu batsa a cikinsa. Ina alfahari da ‘ya’yana da sauran yara za su karanta abin da na rubuta kai tsaye ba tare da Ina jin wani nauyi ba.

To Madalla. Mun gode.
Ni ma na gode sosai.

By Editor