Daga CMG HAUSA
Babban sakataren hukumar raya ƙasa da yin kwaskwarima ta kasar Sin Zhao Chenxin, ya bayyana cewa, ƙasar tana da kwarin gwiwa kuma tana cike da imanin cimma burinta na samun ci gaban tattalin arziki a shekarar bana wato 2022.
Jami’in ya ƙara da cewa, za a daidaita tasirin da yaɗuwar cutar COVID-19 ke haifarwa ga ƙasar, kuma tattalin arzikin ƙasar zai ci gaba da samun bunƙasuwa cikin sauri kamar yadda yake a baya.
Zhao Chenxin ya ce, ya dace a ƙara kyautata manufofin da abin ya shafa domin daƙile sauye-sauyen da ake fuskanta, ta yadda za a tabbatar da ci gaban tattalin arziki a ƙasar ta Sin.
Mai fassarawa: Jamila daga CMG Hausa
