Bankin Access zai rikiɗe zuwa babban kamfani nan da watan Mayu

Daga AMINA YUSUF ALI

Rahotanni da aka samu daga Bankin Access sun bayyana cewa, nan da 1 ga watan Mayu mai kamawa za su ƙara bunƙasa harkokinsu i zuwa kamfanin hada-hadar kuɗin ba wai iya banki za su tsaya ba kawai. 

Manajan daraktan Bankin, Herbert Wigwe shi ya bayyana haka a wata takardar sanarwar da kamfanin ya rarraba ga masu hannun jari a bankin. A takardar, ya sanar da canza sunan kamfanin  daga Accass Bank zuwa sabon kamfani mai suna Access Holdings, PIc, ko Access Corporation.

“Wannan canjin zai sa mu bunƙasa daga banki zuwa babbar harkar kasuwanci na Duniya” A cewar Wigwe.

Ya ƙara da cewa, “Access Corporation zai jagoranci kamfanoni da dama a ƙarƙashinsa waɗanda za su cigaba da samar da biyan buƙatar al’umma. Kamfanonin su ne: Rukunan bankuna: (Access Bank Group). Domin a cewar sa tafiyar da bankunan shi ne babban abinda suka fi iya tafiyarwa.

“Amma yanzu sun ƙara ƙawata shi don ƙara burge kwastomomi da sa musu nutsuwa a dukkan rassansu da suke a Nijeriya da sauran rassansu guda 14 da suke a Afirka, Turai da Asiya.”