Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja
Rahotanni daga yankin Arewa maso gabashin Nijeriya na cewa wani sojan ƙasar ya kashe kansa bayan da aka kama shi bisa zargin aiki tare da mayaƙa masu iƙirarin jihadi na ƙungiyar ISWAP.
Wakilin BBC ya ce wata majiya mai kusanci da rundunar sojojin Nijeriya ta sanar da shi cewa lallai sojan na da hannu a wasu hare-hare da aka kai kan wasu al’umomin Jiihar Yobe a cikin makonnin da suka gabata.
Manyan hafsoshin sojin ƙasar sun fara sa ido kan sojan ne bayan da aka kai wasu hare-hare biyu a garuruwan Geidam da Gashua na jihar ta Yobe, kuma daga nan suka fara bibiyar wuraren da yake zuwa cikin sirri.
An kuma kama shi yayin da yake ƙoƙarin tserewa, bayan da ya gane cewa dubunsa ta cika.
Sai dai sojan, wanda ƙwararre ne wajen sarrafa makamai, ya ƙwace wata bindiga a hannun ɗaya daga cikin sojojin da ke rakiyarsa kuma ya kashe kansa duk da cewa an saka masa ankwa a hannu.
A makon jiya wasu waɗanda ake zargi mayaƙan ISWAP ne suka kai wani hari kuma suka kashe aƙalla mutum goma, ciki har da mata.
Wannan harin ya biyo bayan wani harin na daban da aka dasa wani bam wanda ya halaka mutum shida baya ga raunata wasu mutum 19 a jihar Taraba, harin da ƙungiyar ISWAP ta ɗauki alhakin kai shi.
