Daga IBRAHIM HAMISU a Kano
Muƙaddashin Gwamnan Jihar Kano Dr. Nasir Yusuf Gawuna ya jaddada ƙudirin gwamnatin Kano na tabbatar da tsaron rayuka da dukiyoyin al’umma.
Gawuna ya bayyana hakan ne a ranar Litinin, ya yin da tawagar ƙwararru akan tsaro daga makarantar samar da tsaro ta ƙasa ta kai masa ziyara a fadar gwamnatin Kano.
Ya bayyana cewa a ƙoƙarin gwamnatin Kano na inganta tsaro ta faɗaɗa majalisar tsaron ta wajen shigo da hukumomin tsaro da kiran mitin akai-akai don samar da yanayi mai kyau a jiha.
“Kun zo Kano, ɗaya daga cikin jihohi mafi zaman lafiya a Nijeriya, kuma ta samu zaman lafiya saboda irin kula da jajircewa da gwamnanmu ya ke ba ta.”
Ta cikin wata sanarwar da sakataren yaɗa labarai na mataimakin gwamna Hassan Musa Fagge ya sanyawa hannu ya ce gwamnati tana farin ciki da samuwar makarantar kuma za ta haɗa ƙarfi da ƙarfe wajen a samar da ingantaccen tsaro Nijeriya.
A nasa jabawabin babban kwamandan ma’aikatan Alh. Ayodele Saheel Adeleke ya ce masu muƙamin mataimakan daraktoci ne suke suka halacci wannan kwasa-kwasai don gano bambance-bambance da ke akwai na canjin yanayi da ya shafi jihar Kano, domin ɗaukar matakin gaggawa na hikima zai kuma amfani tattalin arziki, da kare rayuwar al’ummar Kano.
Sannan ya gode wa mataimakin gwamna kan tarbar ta musamman da aka yi masu.
Kazalika ya bada tabbacin cewa za su yi amfani da wannan horo wajen inganta tsaro da dabaru na zamani don cigaban Kano da ƙasa baki ɗaya.
