Malagi ya sayi fom na tsaya wa takarar Gwamnan Jihar Neja

Daga MAHDI M. MUHAMMAD a Abuja

Shugaban rukunin kamfanin jaridun Blueprint da Manhaja kuma mai neman tsaya wa takarar gwamna na kan gaba ƙarƙashin Jam’iyyar APC mai mulkin Jihar Neja, Alhaji Mohammed Idris Malagi, ya zavi jam’iyyar inda ya sayi fom na nuna sha’awa da tsayawa takara a zaɓen gwamna a jihar Neja a zaɓen 2023 mai zuwa.

Malagi ya biya Naira miliyan 50 na duka fom na nuna sha’awa da na takara a ranar Laraba a sakatariyar jam’iyyar APC ta ƙasa da aka fi sani da gidan Muhammadu Buhari da ke Abuja.

Sakataren Ƙungiyar Kamfen ɗin Malagi, Barista Bala Marika tare da Alhaji Abdulmalik Muye da Hon. Isah Kutigi, dukan mambobin ƙungiyar kamfen ne ya ɗauki fom ɗin a madadin wanda ya nemi takarar.

Wata sanarwa da ofishin yaƙin neman zaɓen ya fitar a ranar Laraba ta ce, “Malagi, fitaccen zan kasuwan yaɗa labarai kuma mai hulɗa da jama’a, ya nuna sha’awar tsayawa takarar gwamna a jihar Neja a zaɓen 2023 a ƙarƙashin jam’iyyar APC tun daga 2019, kuma ya cigaba da tsayawa takara zuwa ga duk masu ruwa da tsaki a cikin jihar da kuma wajen”.

“Don nuna jajircewarsa a matsayinsa na ɗan jam’iyya mai biyayya, a kwanan baya Malagi ya ziyarci sabon zavavven shugaban jam’iyyar a jihar a Minna, babban birnin jihar Neja inda ya bayar da gudunmawar motocin bas 31 da Naira miliyan 43 domin sauƙaƙa wahalhalun tafiyar da harkokin mulki na ɗaukacin tsarin jam’iyyar a jihar.

“Malagi ya kuma kai wa ’yan gudun hijirar da ke jihar kayan abinci ta hannun gwamnatin jihar bayan ya bada tallafin COVID-19 don tallafa wa ’yan gudun hijira ta hanyar gwamnatin jihar.”

A halin da ake ciki kuma, ɗan takarar gwamnan ya samu ofishin yaƙin neman zaɓe a Minna wanda ke shirin ƙaddamar da shi ranar Asabar.

Malagi, wanda kuma shi ne Kaakaki Nupe, an shirya ƙaddamar da kwamitin gudanarwa domin gudanar da ayyukan yaƙin neman zaɓen fidda gwani na jam’iyyar APC da aka tsayar a wata mai zuwa.

Ziyarar da ɗaya daga cikin wakilanmu ya kai ofishin yaƙin neman zaɓen da ke ƙofar Gabas da ke kusa da hedikwatar INEC ta jihar, a ranar Laraba, ya nuna cewa an kammala shirye-shiryen tunkarar zaɓen.

Har ila yau, an ga tutoci da dama na jam’iyyar APC suna shawagi a gaban ofishin yaƙin neman zaɓen yayin da aka ga rubutun ‘ofishin yaƙin neman zaven gwamna na Malagi’ a saman ginin.

A wata hira da aka yi da shi, wani jigo a jam’iyyar kuma mai sharhi kan harkokin siyasa wanda ya bayyana kansa a matsayin Yunusa Saba, ya yi maraba da sabon sashen.

“Malagi shine na farko a cikin dukkan masu neman kujerar gwamna da ya buɗe ofishin yaƙin neman zaɓe a Minna. Wannan nuni ne na irin kyakkyawar hangen nesa da ya ke da shi na takara da kuma burinsa na tsayawa takarar gwamna,” inji Saba.

Har ila yau, Sakataren ƙungiyar Malagi na yaƙin neman zaɓen gwamna 2023, Barista Bala Marika, ya tabbatarwa da Blueprint ta wayar tarho cewa an shirya komai na fara aikin ofishin.