’Yan bindiga sun yi garkuwa da Maigarin Rijana

Daga IBRAHIM HAMZA MUHAMMAD

Wasu da ake kyautata zaton ’yan bindiga ne sun yi garkuwa da Maigarin Rijana, Alhaji Ayuba Dakolo Ayuba, a gonarsa da ke yankin Ƙaramar Hukumar Kachia a Jihar Kaduna.

Garin Rijana dai yana kan babbar hanyar Abuja zuwa Kaduna, kuma yana kusa da tashar jirgin ƙasa, sannan ba shi da nisa da inda ’yan bindiga suka dasa wa fasinjojin da ke cikin jirgin ƙasan Abuja zuwa Kaduna bom kwanan baya. 

Kamar yadda majiyar Blueprint Manhaja ta shaida, ta ce, an yi garkuwa da Maigari Ayuba ne da safiyar Alhamis lokacin da ya je duba gonarsa a bayan gari, amma sai da rana tukunna labari ya bazu a gari. Majiyar ta qara da cewa, mutane sun ga isowar jami’an sojoji a yankin dajin da ke garin kuma sun kewaye garin.

Majiyar ta kuma ce, ‘yan bindigar ba su kai wa mutanen garin hari ba, saboda talakawa ne, amma satin da ya gabata sun yi garkuwa da wani ɗan ƙauyen, inda suka buƙaci abinci da giya a matsayin fansarsa.

Majiyar ta buƙaci gwamnati da ɓangarorin jami’an tsaro da su ninka ƙoƙarinsu wajen tsare tabbatar da tsaro a hanyar, musamman yadda Musulmai za su riƙa zirga-zirgar koma wa garuruwansu, don gudanar da shagulgulan Ƙaramar Sallah bayan azumin Ramadan.

Wani babban jami’in gwamnati da ya tabbatar da afkuwar lamarin, a lokacin da ya ke nuna rashin jin daɗinsa, ya ce, su na kan duba lamarin, kuma su na ƙoƙarin ganin sun shawo kan matsalar cikin kwanciyar hankali.