Bikin sallah: ’Yan ta’adda na shirin tada bomabomai – DSS

•Za su kai hari a masallatai da wuraren shaƙatawa

Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja

A daidai lokacin da ya rage kwana kaɗan al’ummar Musulmi su gudanar da shagulgulan bikin Ƙaramar Sallah a Nijeriya, Hukumar ‘Yan Sandan Farin Kaya (DSS) ta ankarar da ‘yan Nijeriya kan wani makirci da suka gano da wasu ɓatagari ke shirin aikatawa a lokacin bukukuwan sallah da bayan sallah.

Hukumar DSS ɗin da kanta ta ce ta gano cewa, wasu miyagu suna haɗin gwiwa domin saka bama-bamai a wuraren ibada, wuraren shaƙatawa da wasu gine-gine masu muhimmanci yayin bikin sallah.

Don haka hukumar ta buƙaci masu wuraren da al’umma ke taruwa su ƙara taka-tsan-tsan don samar da tsaro, yayin da ita kuma da sauran hukumomin tsaro za su ɗauki dukkan matakan daƙile harin ‘yan ta’addar.

Kakakin DSS Peter Afunanya, cikin sanarwar da ya fitar a ranar Talata ya ƙara da cewa ɓatagarin na neman mayar da ƙasar tamkar kafin 2015 lokacin da ake saka bama-bamai a wasu wurare a ƙasar.

“Duk da cewa an samu rahoton afkuwar abubuwan kamar hakan a wasu sassan ƙasar, hukumar ta gano shirin da wasu ɓatagari ke yi na haɗin gwiwa don kai hare-hare kan wasu muhimman gine-gine; wuraren da mutane ke taruwa kamar wurin ibada da wuraren shaƙatawa musamman lokacin bikin sallah da bayan sallah.
“Niyyarsu shi ne cimma wani burinsu da kuma saka tsoro a zukatan ‘yan ƙasa. 

“Don haka hukumar na kira ga mutanen da suka mallaki wuraren da su yi taka-tsan-tsan don kare afkuwar hakan, su tanadi matakan tsaro.” 

Hukumar ta DSS ta ce ba za ta yi ƙasa gwiwa ba domin ganin ta samar da tsaro ta hanyar haɗin gwiwa da sauran hukumomin tsaro don tabbatar da cewa mutane sun cigaba da rayuwa cikin lumana. 

Ta kuma shawarci al’ummar ƙasa su cigaba da gudanar da harkokinsu na yau da kullum kamar yadda suka saba.

Mayaƙan Boko Haram sun yi ƙaurin suna wajen kai hare-hare a masallatai da maja’mi’u tsakanin 2014, inda suke dasa bama-bamai da nakiya don tashi da mutane a kasuwanni da sauran wuraren cunkoson jama’a.

Hare-haren ya fi ƙamari a Arewa maso gabashin Nijeriya da Arewa maso Yamma a wancan lokacin.

Idan za a iya tunawa, Gwamnatin Jihar Kaduna tsakanin Janairu zuwa Maris, 2022, ta sanar da fashewar bam da kuma warware wani a wurare mabambanta a cikin birnin Kaduna, tsohon lamarin da ake ganin kamar yana neman dawowa.

Haka zalika, rahotannin tsaro sun tabbatar da cewa ɓarayin daji masu garkuwa da mutane sun ƙulla kyakkyawar alaƙa da mayaƙan ƙungiyar Boko Haram a Arewa maso Yamma da Arewa ta Tsakiya, wanda hakan ya sa suka canja salon hare-harensu.