Sallah: Masu sayar da kaji a Kaduna sun koka da rashin ciniki

Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja

Wasu daga cikin masu sayar da kaji, talo-talo da agwagi a Kaduna sun koka kan rashin cinikin kajin gabanin bikin ƙaramar Sallah ta bana.

Masu sayar da kajin sun nuna damuwarsu a hira mabanbanta da Kamfanin Dllancin Labarai na Ƙasa (NAN) ta yi da su a ranar Talata a Kaduna.

Sun ce lamarin abin damuwa ne matuƙa, duk da cewa suna da kyakkyawan fatan ganin canji da zarar ma’aikata sun samu albashin watan Afrilu.

Wakilin NAN wanda ya ziyarci fitacciyar kasuwar sayar da kaji a Kantin Koli a Babbar Kasuwar Kaduna, ya hangi mutane da dama suna cinikin kajin.

Kabiru Yunusa, wani mai sayar da kaji, ya shaida wa wakilin NAN cewa duk da cewa farashin kajin ba qaruwa ya yi ba, babu ciniki a yanzu.

“Ana sayar da kaza tsakanin Naira 2500 zuwa Naira 4000 bisa la’akari da nauyin ta.
“Kaji masu saka ƙwai kuma tsakanin Naira 1500 zuwa Naira 2000 ne kuɗinsu, kajin gidan gona  kuma farashinsu yana kamawa daga Naira 2500 zuwa Naira 4000,” a cewar Yunusa.

A ɓangarensa, Jamilu Abubakar mai sayar da talotalo ya ce ya ɗan samu cinikin kaji saura na talotalo.

“Talotalo sun fi tsada, ana sayar da madaidaici tsakanin Naira 9000 zuwa Naira 15000.

“Wannan ba sabon abu ba ne, mutane su kan zo sayayya ko da ranar jajiberin sallah ne, don haka muna dakon zuwansu,” in ji shi.
Baya ga kasuwar, wakilinmu ya tuntuɓi wasu da ke sayar da kajin a kasuwar Kawo.

Hajiya Fatima Mohammed, wacce ke sayar da kaji a Unguwar Sabon Kawo cewa ta yi ita kam bana Alhamdullah, ta ce ta sayar da kusan rabin kajin da ta saka, domin bana yawancin masu kiwon kajin ba su yi ba saboda yana yin rayuwa.

Ta ce farashin kajin nata yana kamawa daga Naira 2500 zuwa 4000, kuma tana sa ran kafin ranar sallah kajin na iya ƙarewa.
“Alhamdullilahi, mutane sun fara sayan kaji babu laifi na sayar da dama kuma ina fatan kafin ranar sallah za a iya saye su baki ɗaya,” in ji ta.

Hakazalika, wani mai sayar da kaji a kasuwar Kawo Kaduna mai suna Malam Sani Mohammed ya ce shi ma ya fara sayar da kajin amma dai ba kamar bara ba, yana mai cewar abubuwa sun canja a ƙasar ta yadda ba kowa zai iya sayan kajin ba.

Amma ya ce yana fatar za a iya samun sauyi zuwa ƙarshen wata idan mutane sun karɓi albashi.

“Rayuwa ta ƙara tsada, ba kowa zai iya sayan kaji ba, amma muna fatan za a samu sauyi bayan an samu albashi a ƙarshen wata,” a cewarsa.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *