Ƙaramar Sallah: Yadda jama’a ke kokawa a Gombe

Daga MOHAMMED ALI a Gombe

Yayin da ake shirin yin ƙaramar sallah a jibi Lahadi ko kuma Litinin idan Allah ya kaimu, al’ummar kuma sai kururuwar rashin wadata suke ta fama da shi:

“Mu dai wannan sallah sai dai a hankali. za mu dai gode wa Allah kawai da Ya kawo mu lafiya. Amma mu talakawa, a wurin mu ba mu da wata, gwamnati ta cuce mu”,  a ta bakin wani bawan Allah kenan a cikin garin Gombe a lokacin da wakilin mu ya yi zagaye don jin yadda jama’a suke shirin sallah ƙarama.

Wani malamin makarantar LEA dake Unguwar Bogo, Malam Saidu, ya ce shi bai tava ganin sallah da ta zo a lokacin da jama’a suke fama da talauci ba, kuma a cewar shi, “gaba ɗaya masu gudanar da tattalin arzikin ƙasar nan, su tashi tsaye saboda abubuwa sun kai intaha.”

Shi ko Baba Yakubu na Unguwar Jekadafari a birnin Gombe cewa ya yi, “lamarin sai dai mu gode wa Allah kawai, amma ba ma cewa komai saboda wannan matsi da takura na rashin kuɗi. Wallahi, muna cikin tashin hankali mu dai mun zuba wa Allah ido kawai amma ba wannan gwamnatin Baba Buhari mara tausayi ba.”

Yunusa Garba na Unguwar Nasarawa, ya ce shi da wasu da dama ba za su iya ɗinka wa yaran su kayan sallah kamar yadda suka saba a baya ba, yana mai cewa “babu abin da yake cikin ran talaka yanzu, banda abin da zai ci kawai, idan ma ya samu. Kai Allah ya sauƙaƙa amin.”

Wani malamin makarantar Allo, Malam Isa Hudu, cewa ya yi komai na zuwa ne dai dai da zamani, kuma “dole mu rungumi ƙaddara mu yi ta addu’a sai Allah ya kawo mana sauqi.”

Wata Bayarrabiya mai sana’ar sayar da abinci a tsohuwar kasuwar Gombe wadda ake ce mata Alajah Yawo, nuna ɓacin ranta ta yi akan tsadar kayan abinci da na girke-girke waɗanda suka yi  hauhawar gwauron zabi. A ta bakinta, “wallahi muna cikin big problem (wato babbar matsala), saboda komai sun yi tsada, ba mu yi ɗinkin yara ba, sai shikafa kowai.”

Wani mai wanki da guga a Unguwan Tunfure, Idris Musa, shi laifin Gwamnatin Shugaba Buhari yake gani inda ya furta cewa “babu wani tantama wannan gwamnatin ta Buhari ta gaza ta fannoni da dama. Ga tsadar rayuwa ga ba tsaro, ba ruwa, kai babu wani abun moriya a wannan gwamnatin. Na rantse gara gwamnatin da ta shuɗe ta Jonathan (tsohon shugaban ƙasa, Goodluck Jonathan) sau dubu. kai, ko Badlok Jonathan ne ya dawo, za mu zaɓe shi,” a cewarsa.

Jama’a da dama dai suna ganin wannan sallah ta zo musu ba shiri saboda rashin kuɗi, kuma yawancin mutane sun ɗora laifin taɓarɓarewar tattalin arzikin ƙasar ce akan Gwamnatin Shugaban Ƙasa Muhammad Buhari wanda a cewar su, “ba ta tsinana mana komai ba.”