Gwamnan Zamfara ya warware rawanin sarakunan Zurmi da Ɗansadau saboda ta’addanci

Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja

Gwamnan Jihar Zamfara, Muhammad Bello, Matawallen Muradun, ya sanar da sauke wasu manyan sarakunan jihar guda biyu da Magajin Gari guda, saboda samun su da hannu wajen ayyukan ta’addancin da suka addabe jihar.

Sanarwar da Gwamnan Jihar Bello Matawalle ya gabatar ta ce, an sauke Sarkin Zurmi Atiku Abubakar da na Ɗansadau Hussaini Umar saboda yadda rahotan binciken da aka yi ya tabbatar da laifi akan su.

Sanarwar da ke ɗauke da sanya hannu Zailani Bappa, mai magana da yawun gwamnan ta ce an kuma sauke Suleiman Ibrahim Ɗanyabi a matsayin Magajin Garin Birni Tsaba.

Sanarwar ta ce an ɗauki matakin sauke sarakunan ne bayan taron majalisar zartarwa wanda Muƙaddashin Gwamnan Jihar Hassan Nasiha ya jagoranta wanda ya amince da shawarwarin wani kwamitin bincike da ya gano hannun waɗannan sarakuna cikin matsalar tsaron da ta addabi jihar.

Kafin dai wannan lokaci an dakatar da waɗannan sarakunan daga aiki saboda zargin da ake musu.