Babu abinda ya haɗa kuɗin fom na APC da rashawa – Abdullahi Adamu

Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja

Shugaban Jam’iyyar APC na Ƙasa, Sanata Abdullahi Adamu ya bayyana cewa babu abinda ya haɗa kuɗin fom ɗin takarar APC da rashawa.

Adamu ya bayyana hakan ne cikin wata hirar bidiyo da Muryar Amurka ta yi da shi, inda yake mayar da martani kan cece-kucen da mutane ke yi dangane da ɗan karen tsadar da fom ɗin shiga takarar neman kujeru a jam’iyyar APC.

A martanin shugaban, ya ce ‘kujerar Shugaban Ƙasa ba abin wasa ba ce, ba kuma kujerar sarkin gari ba ne.”

Ya ce duk ɗan takarar da ba shi da masoyan da za su iya haɗa masa Naira miliyan ɗari, to ko alama bai cancanci fitowa takarar shugaban ƙasa ba.

A cewar sa, Jam’iyyar APC ita ce kowane ɗan takara ke ganin ci a kusa, kuma ita ce ke da tabbasa, domin” ‘jam’iyyun suna suka tara,” in ji shi.

Shugaban jam’iyyar ya sake bayyana cewa duk wanda ba zai iya ba ko magoya bayansa ba za su iya ba to ɗan tasha ne mara amfani, har ya misalta hakan da karen siyasa,  a cewarsa.

Adamu ya bayyana cewa Naira miliyan 20 ya sayi fom ɗin tsayawa takarar shugabancin jam’iyyar APC, wanda a baya 500,00 ne, don haka dole duk mai so ya biya abinda aka gindaya.

Ya kuma jaddada cewa ‘babu abinda ya haxa fom ɗin APC da rashawa,” kamar yadda mutane ke cece-kuce a kai.