Ƙasar Sin ta miƙa wasu takardun amincewa da yarjejeniyoyi biyu ga ILO

Daga CMG HAUSA

Wakilin din-din-din na ƙasar Sin a ofishin MƊD dake birnin Geneva, da sauran ƙungiyoyin ƙasa da ƙasa dake kasar Switzerland Chen Xu, ya mika wa babban darektan hukumar Ƙwadago ta Ƙasa da Ƙasa wato ILO a taƙaice, takardu guda biyu, game da amincewar da ƙasar Sin ta yi da Yarjejeniyar Aikin Tilas ta shekarar 1930 mai lamba 29, da ta Kawar da Yarjejeniyar Aikin Tilas ta shekarar 1957 mai lamba 105.

Yarjejeniya ta 29 da ta 105, na cikin muhimman yarjejeniyoyi 10 na ILO, kuma su ne dokokin ƙasa da ƙasa mafi mahimmancin a fagen kawar da aikin tilas.

A watan Afrilun bana, aka yanke shawarar amincewa da manyan yarjejeniyoyin biyu, a yayin taro karo na 34, na zaunannen kwamitin majalisar wakilan jama’ar ƙasar Sin karo na 13.

A ko da yaushe, gwamnatin ƙasar Sin tana adawa da aikin tilas, kuma amincewar ta da wadannan yarjejeniyoyin guda biyu da kanta, ya kara nuna tsayuwar daka da gwamnatin ƙasar Sin ke yi, game da kare haƙƙi da muradun ma’aikata, da adawar ta, da ma yaki da ayyukan tilas.

Mai fassara: Bilkisu Xin