An buɗe bikin fina-finai na ƙasa da ƙasa karo na 12 na birnin Beijing

Daga CMG HAUSA

A yau Asabar ne aka buɗe bikin nuna fina-finai na ƙasa da ƙasa karo na 12 a nan birnin Beijing.

Shen Haixiong, mataimakin shugaban sashen kula da harkokin faɗakar da al’umma na kwamitin tsakiya na JKS, kuma shugaban babban rukunin gidan rediyo da talabijin na ƙasar wato CMG, kana shugaban kwamitin shirya bikin fina-finai na ƙasa da ƙasa karo na 12 na birnin Beijing, ya gabatar da jawabi, tare da sanar da buɗe bikin.

Taken bikin fina-finan na wannan shekara shi ne “Zuciya ɗaya, aikata na haƙiƙa”, wanda kuma ke gayyatar masu aikin shirya fina-finai daga duk duniya da su haɗa kai, don amfani da sabbin yanayi, da sabbin sha’awa wajen zana wani tsarin ci gaba mai ban mamaki.

A bikin na bana, babban sashin gasar bikin fina-finai na “Tiantan Award” da aka kafa, ya jawo jimillar fina-finai 1,450 a duniya baki ɗaya da aka yi wa rajista, adadin da ya ƙaru da kashi 63% idan aka kwatanta da na bara.

Shen Haixiong

Daga cikin su, akwai fina-finan ƙasashen waje 1,193 da suka fito daga ƙasashe da yankuna 88.

A ranar 20 ga watan Agustan nan ne za a rufe bikin nuna fina-finai na ƙasa da ƙasa karo na 12 na birnin Beijing, lokacin da za a ba da babbar lambar yabo guda goma ta “Tiantan Award”.

Mai fassara: Bilkisu Xin