Sin ta sanya wa Mataimakiyar Ministan Sufurin Ƙasar Lithuania takunkumi

Daga CMG HAUSA

Kakakin ma’aikatar harkokin wajen ƙasar Sin, ya sanar da ƙaƙaba wa mataimakiyar ministan sufuri da sadarwa na ƙasar Lithuania Agne Vaiciukeviciute takunkumi.

Hakan dai ya biyo bayan ziyarar da jami’ar ta kai yankin Taiwan, lamarin da ya keta alfarmar manufar ƙasar Sin ɗaya tak a duniya, tare da tsoma baki cikin harkokin gidan ƙasar, da keta hurumin mulkin kai, da tsaron yankunan ƙasar Sin.

Takunkumin da ƙasar Sin ta kakabawa Vaiciukeviciute, ya haɗa da dakatar da dukkanin wata musaya, tsakanin ɓangaren Sin da ma’aikatar da jami’in ke wakilta, da kuma jingine duk wata haɗin gwiwa da musaya da Lithuania, a fannonin sufurin hanyoyin mota na ƙasa da ƙasa.

Fassarawar Saminu Alhassan