Za a ƙaddamar da gasar Super League a Afirika

Daga MAHDI M. MUHAMMAD

Shugaban hukumar ƙwallon ƙafar Afirika, Patrice Motsepe zai ƙaddamar da gasar Super League ta ƙungiyoyin ƙwallon ƙafar Afrika, tare da alƙawarin dala miliyan ɗari ga ƙungiyoyin nahiyar.

Tun da shugaban hukumar ƙwallon ƙafar duniya, FIFA, Gianni Infantino ya bada shawarar gasar a farkon shekarar 2020 ne ake ta shiri tare da ƙoƙarin tsara gasar, kuma babu irin turjiyar da makamancin wannan yunƙuri ya gamu da shi a Turai cikin shekarar da ta gabata.

Ƙungiyar ’yan wasa a Afrika ta Kudu ce kawai ta soki wanna shiri a wata sanarwa da ta fitar a wannan mako, inda ta ce, wannan gasa, idan aka fara ta, za ta yi mummunan tasiri a kan ƙwallon ƙafar ƙwararru a Afirika ta Kudu.

Motsepe ya yi ikirarin cewa idan har aka fara wannan gasar ta Super League, za ta bai wa ƙungiyoyi damar biyan manyan ’yan wasa albashi dai-dai da yadda ake biyan na Turai, lamarin da zai sa su rage ɗokin ƙetarawa.