Ƙasashen da suka kai matakin ‘yan 16 a gasar kofin Euro 2024

Spread the love

Tawagogin ƙasashe 6 sun samu gurbin kaiwa matakin ‘yan 16 a gasar kofin Turai wato Euro, da ke gudana a ƙasar Jamus.

Tawagogin ƙasashen Jamus da Sifaniya da Portugal da Italiya da Birtaniya da kuma Switzerland ne suka samu nasarar tsallakawa zagayen.

Italiya dai ta samu gurbin ne bayan da aka tashi kunnen doki 1-1, tsakaninta da Croatia a karawar da suka yi a cikin daren ranar Litinin.

A yanzu dai Italiya da ke kare kambin wannan gasa, za ta barje gumi ne da Switzerland don neman gurbi a matakin daf da na kusa da na ƙarshe a gasar.

Ita kuma Ingila duk da cewa bata kammala wasanninta na rukuni ba, amma nasarar Sifaniya kan Albania a rukunin B, ya ƙara taimaka masa wajen kaiwa wannan matakin.

By ukarofi