Hada-hadar kasuwar ‘yan wasan ƙwallon ƙafa

Spread the love

Manchester United na fatan sake sabon kwantiragi da Erik ten Hag, kafin a fara rangaɗin shirin sabuwar kakar wasa zuwa Amurka, a watan gobe.

Tsohon ɗan wasan Manchester United, Ɓan Nistelrooy, mai shekara 47, sun yi tattaunawa mai armashi kan batun komawarsa ƙungiyar a cikin shirin horar da ‘yan wasa da Ten Hag ke yi.

Ɗan wasan gaba na Sifaniya Joselu, 34, na daf da barin ƙungiyar Real Madrid, bayan da ya samu tayi mai gwabi daga kulub ɗin Al Gharafa, na ƙasar Ƙatar.

Chelsea ta fara tattaunawa da Barcelona, kan ɗan wasan gaba na Sifaniya, Marc Guiu, mai shekara 18.

Chelsea dai ta yi wa Bayern Munich, fintinkau kan sayen Guiu, da ita ma ke muradi.

Ana sa ran Manchester United za ta amince da biyan kusan fam miliyan 40, domin sayen ɗan wasan gaba na Netherlands, mai taka leda a Bologna Joshua Zirkzee, 23, suna kuma tattaunawa da Lille, kan ɗan wasan Faransa Leny Yoro, mai shekara 18.

Man United na fatan sayen Zirkzee, idan ta sayar da ɗan wasan tsakiya na Ingila Mason Greenwood, mai shekara 22.

Eɓerton ma na fatan Manchester United, ta sayi mai tsaron baya na Ingila, Jarrad Branthwaite, mai shekara 18.

Eɓerton ɗin dai na daf da kammala yarjejeniyar sayen ɗan wasan gaba na Senegal Iliman Ndiaye, mai shekara 21 daga Marseille.

Asusun Zuba Jarin jama’a na Saudiyya da ya mallaki ƙungiyoyi huɗu na babbar gasar ƙasar, ya nemi ɗan wasan Arsenal ɗan Ghana Thomas Partey, mai shekaru 31.

Atalanta ta kai tayin fan miliyan 10 kan ɗan wasan Eɓerton Ben Godfrey, yayin da wata ƙungiya da ba a bayyana sunanta ba ta mika tayin fan miliyan 15 kan dan wasan bayan dan Ingila mai shekara 26. 

Eɓerton na daf da ɗaukar ɗan wasan Nijeriya Wilfried Ndidi mai shekaru 27 a kyauta idan kwantiraginsa da Leicester ya kare a mako mai zuwa.

Ɗan wasan gaban Newcastle Yankuba Minteh ya ƙi amincewa da komawa Lyon duk da cewa ƙumgiyar ta Faransa ya amince da ɗaukar ɗan wasan na Gambia mai shekaru 19 a kan kuɗi fan miliyan 40.

Brighton na son ɗauko ɗan wasan Inter Miami ɗan ƙasar Paraguay, mai shekara 21, Diego Gomez.

Crystal Palace na ƙoƙarin caukar ɗan wasan Sunderland ɗan ƙasar Ingila, mai shekara 18, Jobe Bellingham.

Ipswich na tattaunawa da Hull kan cinikin ɗan wasan baya na Ingila Jacob Greaɓes mai shekaru 23.

Bayern Munich na shirin ɗauko ɗan wasan Eɓerton Amadou Onana, mai shekara 22, ɗan ƙasar Belgium, bayan bata musu ran da aka yi a a ƙoƙarinsu na sayen ɗan wasan Portugal Joao Palhinha, mai shekara 28, daga Fulham.

Manchester United na zawarcin golan Bayern Munich dan kasar Jamus Maria Luisa Grohs, mai shekara 23, a matsayin wanda zai maye gurbin Mary Earps na Ingila, wanda ke shirin komawa Paris St-Germain.

Ƙungiyar Al-Hilal ta kasar Saudiyya tana duba yiwuwar ɗaukar wani matashin ɗan wasan gaban Manchester United Alejandro Garnacho, mai shekara 19, wanda a halin yanzu yana Copa America da Argentina.

Arsenal na shirin rasa ɗan wasan Stuttgart Serhou Guirassy, ​​ɗan ƙasar Guinea mai shekara 28 wnada ke son komawa Borussia Dortmund.

By ukarofi