Ciwon sikila ba mutuwa ba ce, inji ƙwararru

Spread the love

Daga NASIR S. GWANGWAZO a Abuja

Ƙwararru a harkar kiwon lafiya sun bayyana cewa, cutar Sikila ko kaɗan ba tana nuna alamun mutuwa ba ce don an kamu da ita.

Sun bayyana hakan, a wani taro da aka gudanar a Abuja; wanda ke ƙoƙarin sauya tunanin mutane a kan wannan cuta tare kuma da yin bikin ranar Sikila ta duniya.

Ƙungiyar ‘Mirror Me’ tare da haɗin gwiwar ‘Gehenesphere’ ne suka shirya taron, wanda ya bayar da haske a kan makomar Kobiro Es- elemo, fitacce kuma jigo a cikin al’ummar da ke ɗauke da wannan cuta ta Sikila.

Babban jami’i na ƙungiya ta ‘Mirror Me’ da mai shirya taron, Daniel Ojo, sun jaddada buƙatar canjawar tunanin al’umma dangane da wannan cuta ta Sikila.

“Cutar Sikila, ba ta ɗaukar hukuncin kisa”, kamar yadda Ojo ya bayyana. Wajibi ne, mu daina kallon masu ɗauke da wannan cuta a matsayin raunana ko kasassu, domin kuwa suna da ƙarfi da kuma juriya, sannan lokaci ya yi da al’umma za ta gane tare da fahimtar hakan.”   

Olunaike, babban mai jawabi a wajen taron; ta goyi bayan wannan furuci na Ojo, inda ta jaddada muhimmancin nuna halayya mai kyau da kuma buƙatar tallafa wa al’ummar da ke ɗauke da wannan cuta ta Sikila. Sannan, ta buƙaci ma’aikatan kiwon lafiya da su kasance masu tausayi da tausasawa tare kuma da nuna taka-tsantsan wajen amfani da miyagun ƙwayoyi a tsakanin marasa lafiya.

“Dole ne mu kawar da tatsuniyar cewa, masu ɗauke da wannan cuta ta Sikila na shan wahala wajen shan magungunansu. “Sannan, masu ɗaukar ma’aikata su ma; dole ne su cire son zuciya da son rai wajen ɗaukar masu cutar Sikila aiki. Domin kuwa ko shakka babu, waɗannan bayin Allah na da dama tare da ‘yanci kamar kowa da kowa”, in ji Olunaike.

Da yake yin nasa ƙarin hasken, Oɓye Ewuge ƙwararren likitan jini a cibiyar kiwon lafiya ta tarayya da ke Keffi ta Jihar Nassarawa, ya jaddada yadda za a magance kamuwa da cutar da kuma kula da masu ita yadda ya dace.

Haka zalika, ya sake jaddada muhimmancin neman kulawar likita, lokacin da ake cikin tsanani da tashin hankali; maimakon dogaro da magunguna kaɗai.

By ukarofi