Ƙungiyar APC Arewa Community ta yi taron ’yan Arewa a Legas

Spread the love

Daga DAUDA USMAN a Legas

A ranar Lahadin da ta gabata ta ƙarshe makon jiya Ƙungiyar APC Arewa Community ta Jihar Legas ta gudanar da taron ’yan Arewa mazauna legas tare da karvar baquncin ɗan takara Shugaban Ƙasa ƙarƙashin jam’iyyar APC mai mulki, Bola Ahmed Tinumbu Jagoran.

’Yan siyasar Nijeriya gabaɗaya sun halicci taron na ƙungiyar a Legas wanda ya aunshi dukkan Hausawa da Sarakunansu da sauran ƙabilu ‘yan asalin Arewacin Nijeriya da shuwagabannin ƙungiyoyi daban-daban da ’yan kasuwa ’yan asalin arewacin Nijeriya mazauna Legas.

Sauran sun haɗa da manyan mawaaan fina-finan Hausa waɗanda suka haɗa da Hamisu Bireka da Ado Gwanja da shahararran mawaƙin manyan ’yan siyasar Nijeriya Kamilu, da manyan ’yan wasan kwaikwayon Nijeriya waɗanda suka haɗa da Daushe da Baba Ari da Bosho da Fati Nijar da sauran makamantansu.

Gwamnan Jihar Kano, Dakta Abdullahi Umar Ganduje da Gwamnan jihar Legas Baba Jide Sanwo Olu da sauran waɗansu jiga-jigan manyan ’yan siyasar Nijeriya sun halicci taron.

By Editor