Ni’imarki, darajarki (2)

Daga AISHA ASAS

Shin uwar gida na da masaniyar zata iya rushe soyayyarta daga cikin zuciyar maigidanta cikin ɗan ƙanƙanin lokaci? Idan har ki ka mayar da lokacin kwanciya lokacin ƙorafi, ko tambayar kuɗi da sauran ababen da ka iya sanya maigida ɓacin rai, hakan zai kawar masa da sha’awa ta wannan lokacin, domin masana sun tabbatar ɓacin rai na saurin kawar da sha’awar jinsin maza.

Tun kina kawar da sha’awarki a lokacin da ki ka ɓata masa rai, har ki kawar da ita gabaɗaya daga zuciyarsa. Hakan zai sa ya mayar da hankali kan kishiyar ki, ko matan banza, ko in mai sauƙi ne ya danƙaro miki kishiya idan ba ki da ita.

Kada mu canza wa darasin namu alƙibla, kamar yadda muka faɗa a satin da ya gabata, ni’ima kan iya ƙaruwa, kuma wasu ɗabi’u na iya disashe ta. Ta hanyar amfani da wasu lafiyayu kuma masu tsafta na daga cikin ababen da masana suka tabbatar suna gyara da kuma ƙara wa mace ni’ima, tun daga dangin abinci zuwa ganye.

Idan muka ɗauki ɓangaren abinci mai gina jiki, za mu tarar akwai abebe da dama da ke aiki wurin ingantawa da kuma ƙara wa mace ni’ima. Haka zalika ta vangaren ganye, da yawa daga cikin sanannun kayan mata da ake haɗawa za a same su kewaye da kayan ganye.

Sanin kayan da yadda ake haɗa su na da matuƙar muhimmanci ga duk macen da ke da buƙata da su, domin ta hanyar haɗa su da kanki ne kawai za ki iya tseratar da kanki daga garin neman ƙiba, a tono rama. Rashin tsafta na ɗaya daga cikin ababen da suka yi katutu a magungunan mata da ake siyarwa, kasancewar da yawa daga cikin masu haɗa su ba su damu da tabbatar da tsafta ba.

Wannan ne ya sa, a sati mai zuwa, shafin kwalliya zai kawo wa masu karatu wasu daga cikin ababen da za a iya haɗawa don samun ƙarin ni’ima, hakan zai ba wa mata damar haɗawa daga gida.