Ajizancin namiji a zamantakewa

Daga AMINA YUSUF

Barkanmu da sake haɗuwa a wani sabon makon a shafinmu na zamantakewa na jaridarmu mai farin jini ta Blueprint Manhaja. A wannan makon, muna tafe da bayani a game da ajizancin za namiji a gidan aure.

Kodayake Hausawa sun ce, “Ɗan adam tara yake, bai cika goma ba”, amma a ɗabiar mace, tana ganin dole namiji sai ya cika wasu siffofi sannan yake iya zama namijin gaske.

A duniyar ‘yanadamtaka ma gabaɗaya, ana tunanin cewa namiji wani jarumi ne wanda ba shi da naƙasu ko ɗaya. Kuma kowacce mace fatanta ta auri cikakken namiji mara naƙasu. Wato wanda yake da kusan dukkan waɗannan:

Yana da kyau, yana da kuɗi, yana da ilimi, ƙaƙƙarfar ne, yana da kyawawan halaye, ya iya nuna soyayya, yana sonki sosai, yana girmama iyayenta, mara shaye-shaye, mai zaman gida da ba ya zuwa majalisa, mai dawowa da wuri, mara kula mata ko manemin mata, mai kyauta, mara hana fita unguwa, mara wulaƙanci, wanda zai barki ki yi aiki ko karatu, mai jin maganarki, mai lallashi, wanda ba mafaɗaci ba, da sauran dai duk wani hali na mijin kirki.

Sai dai kash! Waɗannan halaye mawuyacin abu ne, ko ma abinda ba zai tava yiwuwa a samu a wajen namiji guda ɗaya ba. Sai dai akan samu namijin da zai iya haɗa 4 ko biyar ko shida ko sama da haka a waɗannan halaye, ba dai ya haɗa dukkansu ba.

To amma abinda mata suke yi wajen zaɓen mijin aure, suna nema su samu irin wancan namijin da ba ya taɓa samuwa sai a duniyar hasashe ko kuma a finafinai ko kuma a ƙagaggun labarai. Ko a cikin almara.

Idan namiji ya kasance mai dukiya mai ilimi, mai kyauta, ba ya neman mata ko shaye-shaye, wataƙila kuma ki same shi da girman kai, da wulaqanta ki da iyaye ko ko wani abu.

Haka za ki iya samun namiji natsattse mai ilimi, mai iya lallashi, mara shaye-shaye, mai girmama iyayenki, amma sai ki same shi kuma talaka ko mai kuɗin mara kyauta.

Abin dubawa dai shi ne, kowanne namiji da irin naƙasunsa. Kuma wannan abu ya faro tun a tarihi tun zamanin kakanmu Annabi Adamu, da Allah ya ba shi komai da komai ya ajiye shi a gidan Aljannah amma sai ya aikata abinda Allah ya hane shi, ya ci ɗan bishiya. Don haka, kamala ta Allah ce kawai.

Hakazalika, duk yadda za ki kalli miji ko saurayin ƙawarki, to tabbas akwai wani naƙasu a tattare da shi, bayan wannan ƙyale-ƙyalin halayyar da kike gani a waje take ruɗarki.

Watakila kuɗin da mijinta yake da shi, kina ganinta tana fantamawa, wataƙila shi kaɗai take jin daɗi a gidan auren. Wataƙila neman mata yake, wataƙila ƙungurmin jahili ne, ba abinda ya sani a shari’ar musulunci, wataƙila ma har duka yake mata.

Ke kuma ga shi Allah ya ba ki miji mai kuɗi, mai ilimi, mai addini, mara neman mata, amma kina hangen na ƙawarki kawai saboda yana sakar mata kuɗin fiye da naki.

Haba ‘yaruwa, ki yi haƙuri ke ma da naki mijin da Allah ya ba ki. Zaman Duniya fa ba wajen jin daɗi ne da’iman ba. Allah ba ya haɗa Miki komai da komai dole a jarraba ko ta wani ɓangaren. Ajizancin mijinki wani ɓangare ne na jarrabawarki.

Kuma ke mai zaɓen miji ba a ce ki zaɓi wanda ƙiri-ƙiri kika gan shi da munanan hali ba, ko naƙasu ko wanda ɗabiarsa ba ta dace da ra’ayinki ba. Amma ki zaɓi wanda kyawawan halayensa suka rinjayi naƙasunsa.

Hakazalika, a zaɓi dacewar halayya fiye da komai. Ki zaɓi wanda halinki zai tafi da nasa. Kada ki zaɓi mutum a kan zato zai canza bayan aure. Ban ce ba a samu ya canza ba, amma da matuƙar wuya a ce namiji yana da wasu halaye ko ɗabi’u nasa da ya taso a kansu ya iya canzawa bayan ya yi aure.

Da wuya sosai kam. Kada ki sake ki yaudara kanki. Misali namiji yana da rowa ko bai iya lallashi idan kin yi fushi ba ko ba ya girmama iyayenki da sauransu ki ce za ki aure shi, wai don zai canza bayan auren. Sam kin yaudari kanki.

Kuma abinda za ki fahimta shi ne, ki yi haƙuri da mijinki don ke ma ba ɗarin kike ba. So so ne, amma son kai ya fi. Duk da haka kin san akwai abubuwan da kike da naƙasu a kai, amma aka aure ki a haka. Kuma ake zaune da ke ake haƙuri da inda kike da naƙasu.

Misali ke ‘yar talaka lis ki ce kina son mai kuɗi, shi za ki aura. Ko ke ga ki ba kyakkyawa ba ki ce, sai kyakkyawa za ki aura. To kin ga ai kin yaudari kanki ke ma. Za ki iya samun mijin da kike muradi. Amma kafin ki fara neman namiji wanda yake da komai a kammale cif-cif, ya kamata ke ma ki duba kanki, ki ga ke ma idan kin cika waɗannan sharuɗɗan da halayen?

Sannan abu guda ma da mata za su gane, idan sun gane, kuma sun huta shi ne, aure sa’a ce. Kar ku daɗa, kada ku rage. Kamar yadda Hausawa kan ce namiji ba tukunya ko ƙwarya ba ce da za a ƙwanƙwasa a tantance nagari.

Abubuwan da kike gani na zahiri a tattare da namiji kada ya ruɗar da ke ki yi zaɓen tumun dare. Wasu halayen ba sa taɓa bayyana sai an yi aure, kuma sai zama ya yi zama. Sannan sai zama ya yi zama za ki gane cewa, a ƙarshe dai ba wani abu da zai taimake ki wajen jin dadin zaman aure sai irin halayyar mijinki da dacewar sa da naki halayen/ɗabi’un.

Duk naƙasun mijinki ki rungumi abinki wata ma irinsa take nema. Idan kika ce lallai sai kin canza shi, ke ma kin san ba zaman lafiya. Kada ki manta su fa iyaye da sun riga ki saninsa, kuma haka suka gan shi suka ƙyale. Ke ta ina za ki fara canza mutumin da kika haɗu da shi da haƙoransa 32? Gara ma idan addu’a kike yi wataƙila Allah ya amsa muku ya shirya shi.

Haka idan dai har so kike ki samu miji wanda bai da naƙasu, to sai dai ki yi ta kashe aure kina zaga mazaje. Za ki samu wannan ba shi da naƙasun mijinki na baya, amma kin same shi da nasa daban. Za ki iya rabuwa da marowaci, ki faɗa hannun manemin mata.

Don haka, naƙasun mijinki in dai ba yana cutar da ke a zaman sosai ba, ki ɗauke shi kamar sauran jarrabawoyin rayuwa. Sai dai idan wanda musulunci ya ce kada a zauna da su, ko kuma wanda zai zame miki illa a lafiyarki.

Wannan bayanin maza ma su sani, su ma fa ya shafe su. Yauwa, kada mutum ya ɗora wa kansa buri a irin matar da yake so, wacce sam ba zai tava samu ba sai a fim ko a ƙagaggun labarai. Kai ma ka kula da naƙasunka ka kuma yi tsammanin samun wani naƙasu a kan duk matar da za ka aura.

Kana fahimtar hakan, to kuwa ka samu zaman lafiya madawwami. Da ma kaɗan daga abubuwan da suke kawo matsala a zamantakewar aure, ba ya wuce tsammanin za a samu kaza, kuma ba a samu kazan ba. Kuma ba abu mai ƙara daɗaɗa zaman aure irin fahimtar juna da zaman gaskiya-da gaskiya.

Idan kai ma ka ce za ka duba naƙasun wajen zama da mace tabbas za ka yi ta auri-saki kuma ba za ka tava samun iya buƙata ba. A nan zan tsaya, mu haɗu a mako na gaba, idan Sarki mai kowa da komai ya kai rai.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *