Da Ɗumi-ɗumi: Sarkin Dutse ya riga mu gidan gaskiya

Allah ya yi wa Mai Martaba Sarkin Dutse, Alhaji Dr. Nuhu Muhammad Sunusi CON, rasuwa.

Kwamishinan Ayyuka na Musamman a Jihar Jigawa, Auwal Danladi Sankara ne ya tabbatar da rasuwar sarkin.

Sarkin ya rasu ne a Abuja bayan ya yi fama da gajeruwar rashin lafiya kuma ya rasu yana da shekara 79.

Sakatare na musamman ga marigayin, Wada Alhaji Dutse ya tabbatar wa BBC cewa ana sa ran yin jana’izar sarkin ne a ranar Laraba a Dutse

An haife marigayin a shekarar 1945 a ƙauyen Yargaba da ke Dutse, babban birnin Jihar Jigawa.