Bankuna za su ci gaba da karɓar tsoffin takardun Naira ko bayan ƙarewar wa’adin da ya ƙayyade – Emefiele

Daga BASHIR ISAH

Gwamnan Babban Bankin Nijeriya (CBN), Godwin Emefiele, ya bayyana cewa bankuna za su ci gaba da karɓar tsoffin takardun Naira bayan ƙarewa wa’adin da bankin ya ƙayyade.

Kwanan nan CBN ya tsawaita wa’adin ci gaba da karɓar tsoffin takardun Naira da kwana 10 biyo bayan ƙorafe-ƙorafen ‘yan ƙasa.

Da yake jawabi a gaban Kwamitin Majalisar Wakilai kan sha’anin sabbib takardun Naira, Emefiele ya ce bankuna za su ci gaba da karɓar tsoffin takardun N1,000 da N500 da kuma N200 bayan ƙarewar wa’adin da aka tsayar ɗin.

Ya ce bisa la’akari da Sashe na 20 da ƙaramin sashe na 3 na Dokar CBN na 2007, ko da tsoffin takardun Nairar sun rasa matsayinsu a dokacnce, CBN za ci gaba da karɓar su.

Tun ba yau ba Majalisar ta buƙaci ganin Emefiele amma ya ƙi amsa gayyatarta saboda ba ya ƙasar, inda sai a ranar Talata ya bayyana gabanta.

Da yake yi wa Kwamitin ƙarin haske dangane da matakin sauya fasalin Naira, Emefiele ya ce hakan shi ne tsarin da duniya ke yayi, kuma wajibi ne ya zamana CBN yana kula kuɗaɗen da ake hada-hada da su a cikin ƙasa.