Yawan zance a kafafen sada zumunta ne matsalar Kannywood da ke buƙatar gyara – Shamsu Ɗan Iya

“Ba zan tava mantawa da fim ɗin ‘Kar Ki Manta da Ni’ ba”

Daga IBRAHIM HAMISU, Kano

Shamsu Nasir wanda a duniyar Kannywood aka fi sani da Shamsu Dan’ iya, jarumi ne da ya fito a cikin finafinai masu ɗimbin yawa, daga ciki akwai wani fitaccen fim mai dogon zango ‘Alaƙa’ wanda mai gidansa Ali Nuhu yake shiryawa, A tattaunawar sa da Ibrahim Hamisu a Kano, za ku ji nasarori da kuma tarihinsa a cikin shekara 14 da shigarsa cikin Kannywood. Ku biyo mu:

MANHAJA: Ko za ka gabatar mana da kanka?

SHAMSU: Sunana Shamsu Nasir Ɗan’iya da aka fi sani da Shamsu Ɗan’ iya.

Ko za ka bamu taƙaitaccen tarihinka?


Ni an haife ni a garin Kaduna ne, na tashi a can, a can na yi primary da secondary, daga nan na zo Kano na yi difloma. Bayan na kammala, na yi digiri a ɓangaren aikin jarida, wato ‘Mass Communication’ a Maryam Abacha American University.

Ta yaya aka samu kai a masana’atar fim ta Kannywood?

Na fara ne daga aikin sauti, wato ‘sound engeenire’, daga nan kuma na fara shirya fim ɗina na kaina.

A wacce shekara ka shiga masana’atar ta Kannywood?

Na shiga masana’atar Kannywood a shekarar 2009.

Ko za ka iya tuna fim ɗinka na farko?

Na fara ne da fim ɗin ‘Sa’a’ na biyu, na kamfanin Rasheeda Adamu Abdullahi Mai Sa’a.

Ya zuwa yanzu finafinai nawa ka yi?

Gaskiya suna da yawa, amma ga kaɗan daga ciki: ‘Shakka’, ‘Bani da zavi’, ‘Gamu nan Dai’, ‘Garbati’, ‘Kar Ki Manta da Ni’, ‘Sareena’, ‘Mijin Yarinya’ ‘Aisha’, ‘Kanina’ da sauran su.

Wane fim ne ba za ka taɓa mantawa da shi ba a cikin finafinanka?

Fim ɗin ‘Kar Ki Manta da Ni’, saboda na samu award daban-dadan da shi.

Waɗanne irin nasarori za ka iya cewa ka samu ya zuwa yanzu?

Alhamdu lillahi, na samu nasarori da yawa, daga ciki akwai ‘awards’ na ‘City People’ da Amma Award, sannan na samu rufin asiri, alhamdu lillahi.

Waɗanne irin ƙalubale ka samu ko ka ke samu a Kannywood?

Qalubale ai dole ne a same shi, matuƙar mutum yana raye zai same shi, don haka akwai shi.

Da wa ka ke koyi a masana’atar Kannywood?

Da babban jarumi kuma darakta, furodusa Sarki Ali Nuhu na ke koyi.

Wacce ce budurwarka ta farko?

(Dariya) budurwata ta farko ita ce Zarah.

Ya batun aure fa?

Dangane da aure abinda zan ce shi ne, Ina nan Ina shirin yi nan ba da jimawa ba.

Wane abu ne ke baka haushi a masana’atar Kannywood?

Babban abinda ke ba ni haushi shi ne rashin tsari ga shugabanci.

Me ke sanya ka farin ciki?

Abinda ke sanya ni farin ciki shi ne, in ganni a wurin aiki, an dasa min kamara tare da jarumai da muke shiri da su.

Yaya ka ke kallon fnafinai masu dogon zango yanzu a Kannywood, cigaba ko ci baya?

Ni gaskiya a ra’ayi na a matsayin cigaba nake kallon su.

Wane abu ne ake yi a Kannywood da ka ke ganin ya kamata a gyara?

Abinda na ke ganin ya kamata a daina a Kannywood shi ne, yawan zantuka a ‘social media’ domin da yawansu za ka ga cewa ba su da amfani.

Menene burinka a masana’atar Kannywood?

Babban burina a masana’atar Kannywood shi ne na ga na zama ‘director’.

Mun gode.

Ni ma na gode.