Emefiele ya bayyana gaban Kwamitin Majalisa

A wannan Talatar Gwamnan Babban Bankin Nijeriya (CBN), Godwin Emefiele, ya bayyana a gaban Kwamitin Majalisar Wakilai mai bincike kan batun ƙarancin sabbin takardun Naira.

Kwamitin ya gayyaci Emefiele ne domin jin dalilin da ya sa ake fuskatantar ƙarancin sabbin takardun na Naira a faɗin ƙasa.

Lamarin da ya jefa ‘yan ƙasa cikin wani mawuyacin hali.

Ƙarin bayani na nan tafe…