Ƙungiyar Inuwar Ɗaliban Arewa ta karrama Dakta Askiya Sheikh Nasiru Kabara

Spread the love

Daga MUKHTAR YAKUBU

Ƙungiyar Inuwar Ɗaliban Arewa wato Arewa Student Forum ta karrama fitaccen Malamin Addinin Muslumci kuma Shugaban ƙungiyar al’umma masu buƙatar kawo sauyi ta ƙasa wato NCPC da lambar girmamawa a matsayin sa na guda daga cikin muhimman mutane a ƙasa da suke bayar da gudummawar su ga al’umma musamman ta ɓangaren ɗalibai da kuma ci gaban karatu.

A Lokacin bayar da kambun karramawar da aka gudanar a ofishin sa dake kan titin Zaria a ranar Juma’a 22 ga Agusta 2025.

A Lokacin da yake bayani dangane da dalilin zuwan na su har ofishin malamin domin Karrama shi. Shugaban ƙungiyar inuwar ɗaliban Arewar. Ya bayyana cewar.” Sun yi wannan karramawar ne bisa bincike da suka yi na ayyukan malamin da kuma gudummawar da yake bayarwa wajen ci gaban ilimi tun daga matakin farko har zuwa manyan makarantu , don haka suka ga ya kamata su Karrama shi domin ƙara masa ƙarfin gwiwa wajen gudanar da ayyukan sa na taimakon al’umma.”

Ya ƙara da cewa ” Babu shakka Dakta Askiya Sheikh Muhammad Nasiru Kabara ya cancanta a karrama shi domin ta kowanne fage yana bayar da gudummawar sa ga ci gaban al’umma, walau ta ɓangaren karatu ciyarwa ga masu buƙata da taimakon raunana. Don haka a kullum wannan ƙungiyar tamu take bincike domin gano irin sa don a karrama su yadda za su samu ƙarfin gwiwa wajen ci gaba da ayyukan da suke yi.”

Shi ma da yake mayar da jawabi bayan karrama shi da aka yi. Dakta Askiya Sheikh Muhammad Nasiru Kabara, ya nuna matuƙar farin cikin sa da karramawar da ɗaliban suka yi masa wanda a cewar sa wannan wata manuniya ce da take tabbatar da cewa abubuwan da muke yi na taimakon al’umma mutane suna amfana har ma da ta kai wasu daga nesa suka ga abin da muke yi suka zo don su karrama mu.

Ya ci gaba da cewa ” Duk da ba wannan ba ne farko da ƙungiyoyi da hukuma da kuma ɗaiɗaikun mutane suka fara karrama mu, to Amma wannan abin alfahari ne a ce kungiyar inuwar ɗaliban Arewa sun bamu wannan kambu na Karrama. Ina godiya a gare su da sauran al’umma da suke bada gudummawa tare da masu ƙarfafawa masu bayar da gudummawa kamar dai wannan kungiyar ta ɗaliban Arewa”.

Daga ƙarshe malamin ya yi kira ga ɗaliban da ma sauran al’umma da su mayar da hankali wajen samar wa matasa hanyoyin dogaro da kai da kuma ba su tallafin karatu.

By ukarofi