Ƙungiyar Mafarauta ta buƙaci Gwamna Namadi ya duba matsalolinta a Jigawa

Spread the love

Daga UMAR AKILU MAJERI a Dutse

Kwamandan ƙungiyar Mafarauta ta ƙasa ‘Hunters Forest Security Serɓice’, Alhaji Sale Umar ya bayyana cewa, ba a yin kasuwanci da harkar tsaro, domin aikin tsaro ba na ’yan kasuwa ba ne ya kamata gwamnati ta sake yin tunani akan batun kafa hukumomin tsaro da za su baiwa makarantu, cibiyoyin kiwon lafiya da ɗakunan Shari’a tsaro a Jihar Jigawa.

Kwamandan ya bayyana hakan ne a wata zantawa da ya yi da wakilinmu a Dutse.

Ya nuna damuwarsa akan yadda gwamnati ta danƙa harkar tsaron makarantu a asibitoci, kotuna a hannun kamfanonin ’yan kasuwa, ya ce hakan ya saɓa ƙa’ida, bayanan jadawali na gaskiya.

Alhaji Sale Umar ya ce, aikin tsaro, aiki ne na jami’an tsaro ba a sanya ’yan kasuwa ko kanfanonin ’yan kasuwa, sai dai wadda ya san harkar amma ba wanda bai san harka tsaro ba a ɗauko shi a ba shi harkar tsaro yin haka kuskure ne akwai matsala.

Ya ce, idan gwamnati ta siyasantar da harkar tsaro babu yadda za a yi nasara domin ba ka ɗaukar lauya ka bar shi harkar lafiya, kuma Baka ɗaukar likata ka bar shi harkar tsaro koka ɗauki lauya ka bar shi aikin dafa tuwo aikin likita shi ne ba sa magani, kowa ya sani haka, haka zalika, aikin tsaro sai ma aikacin tsaro.

Don haka ya shawarci gwamna Umar Namadi da ya yi ƙoƙari ya AJIYE kwarya a mahallinta kamar yadda ya ke yi a dukkan ma aikata wajan ganin ya sanyar harkar tsaron ma aikatan a hannun da ya dace, ya kuma buƙaci gwamnati ta sake yin duba akan harkar tsaron makarantun da asibitocin da kotuna domin aikin tsaro na masu aikin tsaro ne

Ya ƙara da cewa, ya sani gwamna Umar Namadi Mutum ne da ya ke bin duk wata ƙai’da wajan aiwatar da abinda ya kenda buƙatar aiwatarwa don haka akwai buƙatar Namadi ya sake tunani saboda aikin tsaro ba a yinsa daka.

Saboda haka ya shawarci gwamna ɗaya tsaya ya yi tunani ya ɗauki waɗanda suka dace wajen yin aikin tsaron amma bayan kasuwaba matuƙar gwamnatin da gaske take yi wajan kula da makarantun, kotuna, da asibitoci, amma wannan hanyar yayin anfani da wasu ƙungiyoyi ko ’yan siyasa wajan harkar tsaron akwai matsala.

Da ya juya wajen batun harkar tsaron ya ce, babu irin gudun mawar da basa baiwa gwamnatin jihar Jigawa wajen harkar tsaron, kuma sune gwamnatin ta watsawa kasa a Ido kuma sune suka fi cancanta wajan yi wa gwamnati aikin tsaron a wuraren da gwamnatin Jihar ta ware amma saboda siyasa aka yi fatali da su gefe ɗaya ba ma ayin maganar su.

Domin sune aka ba su horo irin na soja, da ’yan sanda da sauran manyan kanfanonin tsaro kuma suke da ma aikata ƙwararru SAMADA mutun 6000 a kasa waɗanda suke da kwarewa akan harkar aikin tsaro aka ba su horo akan tsaro kuma za su iya horas da wasu amma siyasa ta hana a ba su aikin tsaron makarantun.

“Ni na yi Imani matuƙar gwamnatin Jigawa ta ɗora harkar tsaro kacokan a hannun ƙungiyar mafarauta da ke Jihar Jigawa ba za a taɓa samun wata matsala ba domin aikinmu ne kuma mun iya domin muna alfahari da aikin saboda munsan aikin, saboda muna da kwarewa Akan aikinmu .

Nina sani babu yadda za ka ɗauki ma aikacin tsaro a yau kuma ka bar shi horo a yau kuma Ka tura shi fagen fama alhalin bashi da kwarewa kuma ka sami sakamakon da ka ke buƙata,aikin tsaro na masu tsarone.

Domin komai yana da mahallinsa ya kuma nuna takaicinsa akan yadda gwamnatin ta ɗauki albashin da za ta biya ma aikatan da za su yi aikin tsaron da rashin mashinmanci ya ce kamata ya yi ace akallah dukkan waɗanda zasuyi aikin ace sunada albashi Mai tsaoka duba da yanayin rayuwa saboda zirga-zirga bai kamata a ce albashin su naira dubu Talatin bane.

Ya ƙara da cewa, idan ace sune aka baiwa aikin tsaron sai dai a biya su albashin naira dubu sabain a matsayin albashi mafi ƙanƙanta kamar yadda gwamnatin tarayya ta yi doka, amma albashin dubu talatin ba zai magance komai ba domin jini baya maganin ishirwa, akwai buƙatar gwamnati ta sanya ido ta yi gyara.

Ya ƙara da cewa, waɗanda aka ɗauka aikin ba za su iya aikin ba saboda albashin ya yi kaɗan domin sunada buƙata kamar kowa kuma suna da iyali da iyaye, kuma albashin da aka yanka masu ba zai iya biya masu buƙata ba.

Idan ka juya wajen iya aikinmu ba wai ina zuga kai naba duk Nijeriya babu wanda bai san mu ba saboda ƙwarewarmu ta aiki kuma ba bu wanda bai san irin gudun mawar da muke bayarwa ba a fuskar tsaro a faɗin Nijeriya.

A gefe guda, ya buƙaci gwamnatin Jigawa ta taimaka masu wajan ɗaukar nauyin mutanensu da suke zuwa gidan Soja da ’yan sanda domin samun kwarewa akan aikinsu, ya koka akan yadda SAMADA shekaru biyar suna zuwa aikin horo Amma ko sau ɗaya gwamnatin Jihar Jigawa ba ta taɓa taimaka masu ba saɓanin yadda wasu jihohi suke bawa ’ya’yan ƙungiyarsu gudunmawa idan irin hakan ta taso.

Ya kuma buƙaci gwamna Namadi ya taimakawa ƙungiyarsu da motoci da babura kamar yadda ake wa abokan aikinsu na wasu jihohi waɗanda da sune za su yi anfani wajen inganta ayyukansu na tsaro da suke aiwatarwa a faɗin Jihar ta Jigawa.

By ukarofi